Posts

Showing posts from November, 2017

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE2⃣6⃣ Faruk yayiwa ummy bayanin yanda suka same raihan, ta kalli yusuf "ko kaine kasa mata ciyon kan" faruk ya karb'e zancen da cewa "Ahh haba ummy yayanta yafad'a mana shine ciyon ta" "Toh ka shirya da dare su usaina suje su dubo min 'yata kagayawa fatim sannan ka sanarda uwarka in zata bisu toh inkuma bazataje ba kayi k'ok'arin had'asu a waya dan kowaccen su ta kauda wani tunanin aranta kanajina"    "Eh ummy hakan yayi yanda kikace za'ayi kigayawa 'yan biyu zan sanarda fatim"    Laila yasama tana yayyafa turare, ya gaisheta har k'asa ya duk'a ta shafa kanshi "yadai son" yayi gyaran murya yagaya mata 'yanda sukayi da ummy.         "Ta murmusa ba matsala zanje d'in ay 'yata ce kayiwa fatim waya tin da safe data fita bata dawo ba daga zuwa gidan k'awar ta"   Ya b'ata ...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 2⃣5⃣ Basu bari gwaggo ta gane komai ba sun mata bayanin yanda aka karb'e su, taji dad'i sosai tak'ara da addu'ar Allah yak'ara had'a kansu da dangin mijin na raihan. Raihan ta d'au zafi sosai hakama Yusuf kowannen su yashare wani acewar su an musu laifi dole abasu hak'uri, Raihan kuwa bata da wannan lokacin ko ince bata da wannan tinanin na bashi hak'uri.   Faruk ne yagano da akwai abunda kedamun sa yasa shi agaba dole seda ya mishi bayanin komai, yasauke ajiyar zuciya "gaskiya man kowaccen su tayi kuskure"       Firstly bai kamata amma laila tayi wannan furucin agaban raihan ba domin kamar tafito k'arara ne ta nuna batayi da ita. Secondly bai dace raihan tayi saurin nuna fushin ta agaban amma laila ba kodan kasan cewarta uwa agareka. Thirdly kuma Kaine yakamata ka lallashe raihan cikin sigar yaudara daka kware da ita zaka nuna mata...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 2⃣4⃣ Da murna ta karb'e su tareda musu izinin zama, Yusuf yakoma gun k'afafunta ya zauna yana ta jefawa raihan murmushi, wadda kanta ke k'asa tinda suka shigo, yanuna ta yana dariya. "Ammaty kinganta can fah sewani kame_kame take, kisaki jiki nan gidanku ne"    Laila tayi dariya "gaskiyane ba banbanci da gidanku, sedai kuma son wannan bata fi Amira nah komai ba , ni nazata wata zuk'ek'iya ce takasa 'yata ashe ma dasaura wannan kuwa tayi karatu naganta k'arama"          Ran Raihan ne yab'aci tace wa , surayya tashi muje gida atare suka mik'e tsaye , Yusuf nata soshe soshen kunya "kubari zuwa anjima muwuce" Raihan tabishi da harara. "Nida banyi karatu ba yaza'ayi na zauna gun masu karatu kasake tunani" tana kai nan tasakai ta wuce.    Laila ta rufe baki "aww kaddai ni yarinyar nan zata maidawa magana...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄    © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 2⃣3⃣ Raihan kenan cikin wata atamfa red and black tayi d'aurin d'ankwalin ta simple ta saka sark'a da abun hannu  black ta saka fararen takalmi masu tsini da jaka fara mayafin ma farine gaskiya tayi kyau musamman data saka red lipstick, se zuba k'amshi take , ta wuce d'akin sume itama ta had'u cikin wata jallabiya bak'a tayi rolling abunta 'yen Matan dai sun had'u k'arshen had'uwa ma atare suka sauko downstairs.       Gwaggo da bingyal ne a falo suna kallon MBC Action, ta kallesu "kunyi kyau kamar yaune auren ku, bingyal tace "sis zan biku" sume ta harareta ba inda zamuje dake sekace hauka mu uku agidan sirikai kibari next time aje dake" Raihan ta matso ta jawo ta "kiyi hak'uri kinji yanzu zamu dawo zan biya oasis in siyo miki chocolate bread" murmushi Kawai tayi Allah yakaiku lafiya suka amsa da amin.    ...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 2⃣2⃣ Morning text d'in shi ne yatada ita bacci misalin 7 o'clock, da d'an tsaki ta farka taje tayi brush tajawo wayar tana dubawa. "Fresh flower for you, thinking of you dear now and always, just to say good morning!"    Tab'e baki tayi tajefar da wayar kan gado ta k'ara komawa baccinta, bata farka ba sai 10 tayi hamdala ga ubangiji sannan tak'ara yin brush tareda wanka tasaka kaya Mara nauyi tasauko k'asa domin karyawa, ita kad'ai ake jira lokacin kowa ya halarta, gaisuwa ta mik'a musu sannan bingyal da sume suka gayarda ita, anutse suke cin abincin su kowanne yazuba abunda yake ra'ayin ci, suka k'are akayi addu'a aka sauko kan carpet.        Raihan dame_dame kike buk'ata na aurenki? Dad ne yajefo mata wannan tambayar, kanta k'asa tace "dad inaga muje tareda bro Jidda muyo siyayyar gaba dai" Abdul ya kalleta ...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 2⃣1⃣ Seda gwaggo ta tabbatar ta canza kaya tasaka k'aramin hijabi akan atamfar datake saye d'inkin Niger ya karb'eta sosai powder Kawai ta shafa sai lip gloss, amma tayi kyau sosai, tasauko downstairs tana jin haushin abun Kawai asaka kwalliyar dole, tinda ya hangota ya washe baki yaje tarbota ta zungure mishi hannu tana aika mishi da sak'on harara.    A fuwan ya fad'a tareda langabe kanshi tamkar wani yaro, "meya kawo ka gidan mu? "Nazo ne in miki bayani" "Bana buk'tar bayaninka" "Yakamata mufahimci juna" "Bazan fahim ce kaba" "Raihan kimun adalci" "Kafara yiwa kanka" "Ina son ki fah" "Ban amince da kai ba" "Kiyi hak'uri" "Bazan hak'ura ba" "Raihan zan miki kuka" "Shina fison gani" hannunta ya kamo ya had'e dana shi ...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 2⃣0⃣ Da murna Yusuf yabar gidan yana dariyar mugunta aranshi yace sai ni yusufah namijin duniya na raihanatu bintu Adam ya kyalkyale  da dariya , gaskiya Yusuf bashida tausayi Amira tabani tausayi sosai but shi ko ajikin shi sai ma murnar yake yaci nasara a kanta.     Faruk ya dubesa "anya man akwai zuciya a k'irjinka anya Kanada imani waima kacika cikakken musulmi kuwa" Yusuf ya shure shi "ya isheka ba musulmi bane kafurine original not photo Sat copy"    Faruk yace "koma me zakace wlh bakayiwa yarinyar nan adalci ba ko kunya ma bakaji ba dukda shawarata ce amma yakamata ka lallasheta shine zaka had'a mata harda kiss bayan kasan yana k'ara affection" ka fad'a ya daga itace first kiss d'ina koya tadauke shi ruwanta banda wani case da ita from now, gata nayi mata akan na aure ta bana sonta gwara hakan.      Haka suka cigaba ...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 1⃣9⃣ Alh kabir da Alh Adam sun had'u sun tattauna akan zancen auren 'yayan su sosai suka samu mafita , baza ka iya tantance waye yafi nuna farin cikinsa acikinsu ba , sun tsaida rana nanda sati d'aya za'a turo magabatan Yusuf domin Neman auren ta, da haka suka rabu.    Raihan agaban dad d'in ta yana tambayar ta ko kinsan wani yaro Yusuf, tayi dariya   "ehh dad ay he's my friend na San shi da dad'ewa" dad yace baida wata matsala koh? "Kai gaskiya bayada dad ina ma duk macen da zata aure shi murnan samun miji abun kwatance irin shi" dad yace "shikenan tashi kiyi tafiyar ki"   Bata kawo komai ba atunanin ta zuwan dayake gidan su ne yasa dad yake tambayar waye, tana shiga d'akin ta takirashi a waya times two bai d'aga ba taji haushi tayi jifa da wayar tacigaba da sha'anin ta.       Dad yatara matansa biyu laila da Aisha...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 ©  ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 1⃣8⃣ Yau kam atareda dad d'inta take cin abinci shiyake bata abaki tana wani langab'e kai, mami ce haushi yacikata tace mishi "ya kamata karage shagwab'a yarinyar nan baka San hannun Wanda zataje ba , baka San ko Wanda zata aura zai iya kula da ita kamar yanda kakeyi, sam zaman bazaiyi ar'mashi ba muddin baka nuna mata yau da gobe sai Allah mekake tunani aranar data wayi gari babu mu a dubiya"     Dad yakalleta "naji zan gyara but kisani bazan iya daina kulawa da 'yata ba haka ma nasan a inda na d'orata a tarbiya koba raina zata kulamin da kanta koba haka ba 'yar gidan dady" murmushi kawai tayi jikinta yayi sanyi lokacin data tuna cewa Yusuf ne zab'inta lallai mami tayi gaskiya Yusuf bazai tab'a lallab'ata ba kamar dad, but zata jure komenene.       Yusuf kuwa sai tsare_tsaren auren shi da Raihan yake , yau saura sati d'ay...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 1⃣7⃣ Kwance yake kan katifa yana game da wayar shi faruk ya fad'o kanshi "yane" Yusuf yayi jifa da wayar shi yana haki , tuni faruk ya kyalkyale da dariya.      "Amma dai kai d'an iska ne na bugawa a jarida wannan wani irin iskanci ne zaka fad'o min d'aki ba sallama, sannan kazo kaina kacika d'an iss wlh" faruk yad'auko mishi wayar shi yana mai cigaba da dariya.    Wayar shi ce ta d'au ruri ya duba tareda ware idon shi, ya kalli faruk yasake kallon wayar, faruk yadube sa "kad'aga wayar mana" yad'an shafa sumar shi "I was surprise ne wai Raihan ce ke kirana"     Faruk ya tab'e baki "kana wani surutun har wayar ta tsinke" Murmushi yayi.    "Ba matsala zan kirata but I'm scared fah" Faruk yace don me kuma?   "Na gayawa mamanta cewa ina sonta amma ita ban tab'a gaya mata ba ...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 1⃣6⃣ Mr yusuf S/market. Zaune yake tareda faruk suna lissafin kud'in su atace riba afitarda uwar, faruk ne yaketa murmushi ganin sun samu cigaba sosai yakalli Yusuf yace "Man guys d'in nan fah suna kawo light.     Yusuf ya gyad'a Kai yana cigaba da typing a computer baya son magana kar ya rikece.      Siririyar mace k'irar coca cola tazo gaban Yusuf tana yanga cikin wata shiga maras kyau da ita da 'yar arna dik d'aya.     Faruk kanshi tabashi haushi irin yanda take wani bouncing agaban workers d'in market.     Kujera tajawo tama kanta guri , ogan ko d'ago kanshi baiyi ba , tasamu damar ce mishi Yusuf kabir binji.     "Yes Ina jinki" Ya bata amsa. Ta d'an tabe baki tak'ara tauna gum d'inta tace gurinka nazo da buk'ata.     "Sai kin fad'a" Amsar kenan daya bata. Tace number...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 1⃣5⃣ Gidan prof Isma'il. Gidane babba Wanda ya amsa sunan shi na gida , gidan professor Isama'il kenan mahaifin Amira , prof d'an asalin jiyar yobe state ne kasuwanci ya maidashi Kaduna da sokoto.     Anan ya had'u da shamsiyya mahaifiyar Amira, yayar  laila wato matar uban Yusuf kenan. Shamsiyya mace ce mai mutunci da da'a tanada karamci da sanin meya kamata.      Sam bata so auren prof ba sedan kwai tsarin mahaifinsu ne auren masu kud'i , biyayya tayi ta aure shi bisa tilas badan ranta ya so ba , Sam bata bari yagane hakan ba yanayin biyayyar datake mishi kamar da can ta soshi bare kuma yanzu anyi shekaru atare har ga rabo yasamu.     Kwance take kan cinyar maminta tana mata gyaran gashi se mutsu _mutsu take saboda tsawon gashin har kan duwawun ta.     "Mami Dan Allah kirage min gashin nan wlh yana ...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 1⃣4⃣ Yadad'e tsaye bai iya shiga daga ciki ba , sai da Raihan tamar flashing sannan yasamu k'warin gwiwar shiga a ciki.      Kan wata luntsume miyar sofa ya yada zango yana bin yanayin d'akin da kallo kamar baitaba ganin shi ba. Raihan ta dubesa tayi murmushi , "sannu da zuwa ya hanya"  yad'an sosa k'eya yace.     "Lafiya lau hup kowa lafiya" Tad'an tabe baki "think so" D'ago beauty eye's d'inshi yayi yakalleta wanda tuni ta maida hankalinta ga wayar ta.     Yace da ita "haka ake tarbon bak'o ko ruwa babu ko bakiyi murna da zuwa na ba"     Murna tasake maimaitawa "ina ba gurina kazo ba , Kace gwaggo kazo gayarwa kajirata man seta zo ta tarbeka ni kaga wuce wana" Ya bita kallo lallai akwai aiki agabana babba ni sam ba gurin wata gwaggon dana zo kawai pretending nake.     Gwaggo ce ta ...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ®NAGARTA WRITERS          ASSOCIATION PAGE 1⃣3⃣ Faruk yadafa shi " calm down friend ina da tabbacin komai zaizo yanda akeso" yusuf da jinsa kawai yake yi yace    "how kaji me wannan tace bazata so duk matar da zan aura ba inba Amira bace, wannan ai shi ake kira selfishness" faruk ya furzar da iska yace     "akwai mafita guda biyu dole kayi d'aya ka jefar da d'aya ita kad'aice hanya mafi sauki agareka" Yusuf dake binshi da harara yace...    "c mon kanada shawara amma ka tsaya wani iskanci" faruk ya k'yalky'ale da dariya.      "naji kome kace ba laifinka bane soyayya ce. yusuf ya kaimishi naushi dasauri faruk ya goce yana dariya.       "kagane friend the only solution shine, kodai ka auri Amira ka yafe soyayyar raihan .     kokuma kanemi amincewar Amira akan auren...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE1⃣2⃣ Har k'asa ya duk'a yagaida ummyn shi ta amsa ba yabo ba fallasa tacigaba da kallonta seda yagaji dan kanshi yace "Umma kince kina nemana".    Volume ta rage tace "Eh dadyn ku yabani sak'o gareka ko ince ya aiko ni in b'ata yawun bakina.     Ya shaida min agaya maka lallai wata d'aya ya baka ka fitar da matar aure yagaji da ganinka a haka".    Gyara zama yayi "amma umma ai shi aure lokaci gareshi idan yazo seka ga har yawuce an manta baya basai ansaka min lokaci ba idan yayi da kaina zan kawo muku suruka har gida".   Mugun kallo ta watsa mishi "sannun ka dai sarkin tsari dayake kaine kahaifemu ba. Ni zaka gayawa abinda yadace, muyi kaje da kai har uwar  dake d'aure maka gindi kuyi abinda kukeso tinda seyanda kuka ce za'ayi sakaran yaro mara tunani".   "Haba umma agabana kike zagin mahaifiyata" baki bud...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE1⃣1⃣ karki kuskura wata k'awar banza tabaki shawarar zuwa gurin wani malamin tsibbu dan a karkato miki da hankalin yusuf.     ALLAH yafiki Sanin mekike ji idan kika daure inada yak'inin koda baki samu yusuf ba zaki samu Wanda yafi shi alkhairi agareki.     Amira tak'ara  fashewa da kuka. "Bansan meyasa nake son shi ba inada masoya Wanda sukafishi komai a duniya iya sanina banida wata matsala da namiji zai k'ini meyasa meyasa" tasake fashewa da wani sabon kuka.      Raihan tajata suka Shiga mota seda suka hau titi sannan tace mata "inane unguwar ku" gwuiwa low cost tabata amsa.        Suna tafe tana nuna mata hanya har sukazo gidan , godiya tayiwa raihan sosai raihan tace yiwa kaine.      "karki manta da karanta hailalala a duk lokacin da ranki yasoma b'aci".   "...

FULANIN BIRNI

Image
🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 🔟 Sannu sannu k'awancen raihan da yusuf yafara tsawo yakan zo yajata suje yawon shan ice cream da hutawa . Har ranshi yake jinta but yabar abun kan cewa dan tana Fulani ce haka yake jinsu kamar jininsa. Hakama raihan tad'auke shi kamar Abdul yayanta.     Yau ma kamar Kullum tare suke da faruk sunje wani park , tayi shigar black and red d'in atampa gown ce da akayiwa akaiki da stones sai d'an k'aramun kyalenta data yafa d'an kwalin kuwa dashi tayi ribbon ta tufke kanta se wata red bag da ratsin black.     Tayi matuk'ar kyau se wani kallo yake jifanta dashi.      Tuni faruk yad'ago abokin nashi akan raihan kawai ya kyaleshi ne yana son ganin iya gudun ruwanshi akanta.      Zaune suke kan grasses suna kallo a laptop d'in shi , sukaji anyi sallama bai d'ago ba dan yagane muryarta.     ...

FULANIN BIRNI

🎄FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE9⃣ Wayar shi ce tasoma ring yaduba screen d'in ba name saboda haka suka cigaba da firarsu yaji dad'i sosai raihan batada matsala sai dai tana yawan katse mishi hanzari.      Raihan yakira sunanta tad'ago sexy eye's d'inta yace "zamu iya zama k'awaye? seda ta b'ata fuska sannan tace "eh toh zamu iya but ni fad'a zamu rik'a yi da kai in kana b'atawa Amira ina tausayinta dayawa"      Dariya yasoma "lallai kam zamuyi fad'a dan bata gabana kwatakwata bama itaba kowacce mace ta duniya kece mace tafarko dana fara saurara har naje gurin ta gaskiya ke 'yar baiwa ce" hmm.      "Allah yahad'a mune dan in k'watar wa Amira 'yancin ta in koya maka sonta" . Aranshi yace dama kin taimaka kin koyawa zuciyarki sona zaifimin sauki akan wata Amira tana kallonshi tace.      "mekake sak'awa aranka ? ...

FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 8⃣ Kallonshi tayi dawani murmushi yak'araso gunta tashafa sumar shi , yace     "Ammyta barka da hutawa" Apple ta basa tace   "Lafiya lau dan k'warai Wanda yafi dubu yusufa badai kyau ba ko abaya mata zaucewa suke da kyanka yusufa d'a yusufa bawa yusufa d'an sarkin masar"       Killer smiling d'inshi yayi yana shafa gefen sumar shi. "wannan wankan fah yusuf zance zakaje ne?  yaware ido. "not yet fah Ammyta gurin faruk zanje zamu wani gurin" Ido ta k'ura mishi tana son gane gaskiyar shi , amma yak'i bari suhad'a ido , dariya tayi. " Yusuf k'arya bata maka kyau fah".     Ido yaware yatashi tsaye. "sai na dawo" agurguje yabar d'akin aransa yana mamakin yanda take saurin kamo shi.       Wata royal black lemosine yafito da ita a parking space yashiga.       ...

FULANIN BIRNI

🎄FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 7⃣ Alhaji Adam shine asalin sunan shi daga kebi state. Kasuwanci yamaida shi sokoto a unguwar sama road , nono yake kawowa a kasuwar gandu sannu a hankali sana'ar ta karb'eshi har yafara shigowa da shanun sa , yana sayarwa sari.     Kyawon nonon shi yasaka wani babban mai kud'i agadastawa. D'aukar shi aiki yana kula mishi da shanun shi,      Iya kiyonshi yasaka nonon shanun kyau sosai har suna sarrafashi takowace hanya abun ya bunk'asa yafara yin na kanshi da kanshi , Allah yasawa abun shi albarka ahalin yanzu in kana son yoghurt na k'warai to kasiye Adam yoghurt pure water, ice cream, fura dasauran kayan sanyi sune suka karb'eshi.    Yanada shop sunfi ak'irga ba abunda basayi har nonon rakumi suna kawowa.          Malam bubukar shine mahaifinshi.       Yanada mata d'a...

FULANIN BIRNI

Image
🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE6⃣ Allah yajarabe laila da ciyon Mara saboda haka kwalliya bata biya kudin sabulu ba.    Kabiru kuwa tuni yacire rai da haihuwa yafi alak'anta shi dacewa shine da matsalar , ana haka Aisha tasamu ciki bata gayawa kowa ba seda yayi wata takwas tasame alh kabir tamishi bayani bai wani murna ba acewarshi inda sauran sukaje wannan ma can zaije.      Itake kwantar mishi da hankali da bashi baki harya d'an nutsu suka duk'ufa da addua , Alhamdulillah tahaife d'anta namiji kyakkyawa kamar sauran aka rad'a mishi Yusuf.       Yusuf yatashi hannun laila tana mugun ji dashi akanshi dakowa tana samun matsala ko uwar data haifeshi bata isa ba haka suke ta rigima da ita.       Yusuf yaga gata kala_ kala kowa sonshi yake baiwani samu kunyar d'an fari ba course yazo lokacin da ake bukatar shi.    ...