FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 2⃣1⃣

Seda gwaggo ta tabbatar ta canza kaya tasaka k'aramin hijabi akan atamfar datake saye d'inkin Niger ya karb'eta sosai powder Kawai ta shafa sai lip gloss, amma tayi kyau sosai, tasauko downstairs tana jin haushin abun Kawai asaka kwalliyar dole, tinda ya hangota ya washe baki yaje tarbota ta zungure mishi hannu tana aika mishi da sak'on harara.
   A fuwan ya fad'a tareda langabe kanshi tamkar wani yaro, "meya kawo ka gidan mu?
"Nazo ne in miki bayani"
"Bana buk'tar bayaninka"
"Yakamata mufahimci juna"
"Bazan fahim ce kaba"
"Raihan kimun adalci"
"Kafara yiwa kanka"
"Ina son ki fah"
"Ban amince da kai ba"
"Kiyi hak'uri"
"Bazan hak'ura ba"
"Raihan zan miki kuka"
"Shina fison gani" hannunta ya kamo ya had'e dana shi ki tsaya mu fahimci juna Sam bayadda kike tunani bane, nasan zakice na nuna miki isata ban nemi amincewar kiba na tura magabata na, na karb'i wannan kuskuren, zancen Amira kuma ki kirata kiji dikkan bayanai"
    Da harara take kallon shi "Amira ay nakirata bankuma yarda daku ba nasan tabbas wani shirin ka k'ulla mata dan ka Kawar da tunanina, mena fita, kyau, kud'i, ko ilmi, ko d'aya ban fita ba meyasa kake k'inta ne?
   Ajiyar zuciya ya sauke " kibar wannan zancen so baya duba da su ba kuma sune zasu saka inso mace ba nawa tsarin da banne, kisaka aranki Amira ba mata ta bace kece matar ki karb'i wannan amatsayin kyauta.
    "Naji bazan bijere wa iyayena ba amma kasani sena ramawa Amira abunda kake mata" dariya yayi "how comes ai ke kina sona ba kamar niba da bana sonta"
"Ni bana sonka"
"Ok ki kalleni ki fad'a kuma ki rantse baki tab'a mafarkina ba baki tab'a tunanina ba"
  Shiru tayi ta kasa cewa komai yayi murmushi, yajawo Leda "ga wannan inji ummy suna gaidaki itada Ammaty"
"ina amsawa nagode" yajawo wayar shi yakira ummyn shi, tana d'agawa yace "yauwa ummy ga sirikar taki ta matsamun wai setaji muryar ki" dasauri Raihan ta juyo jin k'aryar dayake mata, ya mik'a mata wayar yana mata gwalo, sallama tayi cikakka ummy ta amsa suka gaisa kowanne yana girmama wani, kamar kar suk'are irin hud'ubar da ummy ke mata atake taji sonta azuciyar ta.
   "Nikam wai me take gaya miki ne? Ta murguda baki "bazaka jiba" ka fad'a ya d'aga ya kamata in wuce, ta kalli ruwan da suke ajiye "waya kawo maka zallar ruwa haka" b'ata fuska yayi k'anwar kice har nace mata ina son zob'o in akwai da indomie tace babu"
Ranta ya b'aci ta k'wala mata kira, da sauri tasauko tana rik'e da Teddy d'in ta, Raihan kuwa ta Shiga mata masifa batareda tajira cewar ta ba, sannan ta bata 15 minute taje ta had'a zob'o  da indomie.
  Amma sis kinsan akwai masu aiki" dasauri yatareda bana cin girkin masu aiki" toh kinji kiyi sauri kar in b'ata miki ra, da kuka taje kitchen ga haushin anyi mata fad'a abunda ta tsana ga kuma haushin k'aryar da ya mata gashi ansata aiki, ta share hawayen fuskarta , tayi murmurshin mugunta dani kake zance wlh sekayi Dana sanin sakani girki.
    Zob'on ta fara had'awa ta zuba k'ank'ara ta maida gefe d'aya ta kunna gas ta dafa indomie wadda taji tarugu sosai, tajera a faranti cikin mintoci k'alilan tafito tana murmushi, Raihan ta tareta tana mata sannu tahaye upstairs tana dariyar mugunta, indomie yafara ci spoon d'aya yayi saurin maida shi aciki, Raihan ta dubesa lafiya? "No bakomai zafi ne da ita" ya bataba amsa zobon kuwa ba inda aka saka sugar salaf tayi shi se uban yaji data cika, haka yadaure yayi spoon uku yasha zob'o bakin shi kamar zaiyi gobara saboda zafin yaji.
    Yacewa Raihan ta turo mishi bingyal ta karb'i tukuicin abinci yayi dad'i sosai, nan sukayi sallama.
  Bingyal kuwa gurin gwaggo taje tasaka baccin k'arya sanin abunda tayi koda taji shigowar Raihan se tak'ara lafewa, Raihan kuwa waya tamishi kan bingyal tayi bacci sedai wani lokacin, murmushi yayi kin kub'uta wannan karon amma bazaki tserewa hukuncin nan gaba ba.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI