FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI. B ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 4⃣0⃣

Muhammad salim shine sunan da aka bawa yaron, sunfi kiranshi da salim se ummy ce ke kiranshi da Muhammad.
Daga shi har maman shi suna asibitin ana kula dasu, sosai yusuf yake hak'uri da danne damuwarsa akan zaman asibitin sedai bashida yanda zanyi , a haka sukayi wata d'aya da sati biyu ya dame faruk akan shifa yana buk'atar matarshi dole faruk yabasu sallama suka koma gida.
   Wata tsohuwa daga binji aka d'auko tana kula da salim tareda nuna wa raihan yanda zatayi wankan jego, kyakkyawar kulawar dasuke samu ta sanya sukayi b'ulb'ul abunsu kamar basuda matsala.
     Bingyal na matuk'ar son salim yusuf ma yafahim ci hakan saboda haka ne yake d'an d'aga mata k'afa akan rainin wayonta, har yakance tafi raihan sonshi.
    Lokacin daya cika shekara d'aya Amira tad'awo Nigeria bayan ta kammala degree na biyu, itace ta had'a mishi birthday na musamman a wani gidan nata sedai tsoro da fargaba sunhanata tinkarar iyayen yaron tana masifar son salim ganin yanda yake kama da yusuf yaron kamar babanshi yake komai iri d'aya sukeyi.
     Da fargaba ta kira yusuf sallama kawai tayi yagane kowace "Amira" ya furta Kalmar unexpectedly "yusuf Ashe zakayi recognising voice d'ina I'm so happy ya uwargida" murmushi yayi lokaci guda yatina rabuwar su da yanda ta kasance "nice" ya furta batareda yasan Kalmar ta fito ba.
    "Nice" kuma ta tambiye kanta "am anyway yusuf I want do me favour".
    "Yes go on" ya bata amsa.
    "Yusuf dan Allah kayarda kabani aron salim na one day na had'a mishi birthday" shiru yayi baice komai ba yana nazarinta seda tace "hello yusuf" sannan yace "kinga zanyi shawara komai na yanke zakijini nagode" dif ya tsinke wayar.
     Yusuf kenan ta furta.
            yasoma canzawa harda godiya.
    Koda yasame raihan da zancen saiyaga tayi murna abun seya d'aure mishi kai "bae are you sure ba damuwa kinsan wancan karon data kiramu kinyi fushi bana son hakan tasake faruwa" fuskarshi ta shafo "bakomai mijina Amira ay maman shi ce koba komai bare muna saka ran nan gaba tashigo gidan nan" hararta yayi "karki sake fad'en wannan nagaya miki".
    Dariya kawai tayi ta kurawa bayan shi ido hawaye masu zafi suke mata sintiri a fuska.
      Da kanshi yakaimata salim gidan su tayi matuk'ar murna da hakan har k'asa ta duk'a tana mishi godiya, yaji dadin hakan kuma ta birgeshi yusuf nason godiya.
    Koda bingyal tazo gidan baya nan, masifa tayita zubawa akan danme za'a bawa wata banzar Amira salim bayan itama ta had'a mishi nashi birthday d'in.
      Baiyi two hours ba taje ta karb'o shi, tazo dashi gidan tahad'a d'an k'aramin decoration komai red colour.
      Koda yusuf yaje k'arb'oshi baya nan sai cemishi tayi ai k'anwar matarka tazo ta karbeshi wai anhad'a mishi nashi birthday d'in a gida , atak'aice dai taso tamun rashin kunya har k'awata taso ta daketa na hanata.
     "Meyasa kika hanata ai da kibari tamata dan banzan duka tinda batada mutunci" hak'uri ta bashi yak'ura mata ido kawai yarasa meyake ji akanta wannan karon baitab'a jin tausayinta ba se wannan lokacin.
       A fusace ya isa ya gida da niyyar zaiciwa bingyal mutunci dama sun saba, koda yayi sallama yasameta a falo ta goya salim tana mishi wasa.
   Sallamar shi ta amsa tana k'ok'arin sauke salim ya dakatar da ita, "No barshi a goyen" haka takeyi duk lokacin daya zo zatayi k'ok'arin bashi d'an shi Sannan ta basu guri.
     "Meya kaiki gidan Amira harda mata rashin kunya? Juyowa tayi "Aww k'arata takai gurinka kenan ashe ta manta cewa kai ba alk'ali bane bare ka yanke mun hukunci, kokuma ta manta cewa nafita iko akanshi".
    "Dan kin fita iko dashi ai bakifi ubanshi iko dashiba shida yakaishi gurin meyasa wai bingyal bakyaji meyasa bazaki bawa mijina respect ba , bana son wannan abun da kukeyi sekutiya sakani ciyon kai nafahimci bakwa k'aunar junanku sekace ba alak'ar komai tsakanin Ku meyasa ne".
    Bingyal tasauke salim tajawo gyalenta tabar gidan.
    "You see ba totally k'anawar nan taki batada behaviors na kirki batada manner ta magana tana komai yanda taga dama a yanda taso idan na mata magana tamun rashin kunya, bakuwa zan lamunci hakan ba kwata_kwata".

ASEEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

Fulanin birni

FULANIN BIRNI