FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 3⃣7⃣

Raihan ta taimaka musu suka gyara gidan da kitchen, ta sako hijabi at d'auko  car key d'in ta tajawo hannun bingyal.
"Ina zakije" cak ta tsaya kana ta juyo fuskarta ad'aure "gidan ubana" murmushin takaici yayi "da kyau idan kinje karki dawo tinda na daki 'yar gold" tattaki tayi har gurin dayake "of course dani ka daka bazan ji komai ba, amma auta ta nuna ta da yatsa idonta fal da hawaye, dubi yanda ka b'ata mata fata idan ku kunsaba da dukan kawo wuk'a mu bamu saba ba" hannunta ya damk'o yayi baya dashi yad'aga d'ayan hannunshi zai mareta sekuma ya dunk'ule shi yasaketa yana ja da baya yana nuna ta da yatsa har yashige restroom d'in shi.
   Taja hannun bingyal sukayi waje lokacin su fatim har sun bar gidan, motarta ta fidda suka Shiga tayi driving d'in su, sunyi nisa a tafiya  bingyal tace "sister baikamata kifito bada izinin saba kuma kidena musayar yawu dashi tinda mijinki ne."
     "Ke rufe min baki, zaman shi mijina bashi zai saka inyi tolerating d'in iskancin shi ba agaban k'annen shi yana disgracing d'ina never" shiru bingyal tayi dan bata da abun fad'a.
    Suna isa gidan bingyal tashiga da gudu ta fad'a kan gwaggo tana rusar kuka, kan ta tanbiyeta lafiya raihan itama ta shigo tana nata kukan, gabaki d'aya suka rikita gwaggo takira sume da tunba.
    Raihan ta musu bayanin meya faru, "amma wlh kin bani kunya raihan wannan itace d'abi'ar dana koyar dake, kinyi masa laifi sannan ki kasa karb'an laifinki, yanzu da kika zo yaji kikayi kokuwa k'arar mijinki kikawo aurenki wata d'aya da kwanaki" raihan ta d'ago rinannun idonta ta kalli yayar tata salma tace "anti dubi yanda ya zane auta fah".
"Rufe min bakinki ita kad'ai ya daka har k'annen shi fah ketaki k'anwar ce bazata bugu ba koh ? Toh wlh maza ki tattara kayanki kibar gidan nan ko minti goma karki k'ara tinda ke kika kawo kanki kitabbatar kin maida kanki, kibashi hak'uri ki karb'i laifinki India kina son shaidar kwarai".
    Haushi yacikata ta kalli gwaggo data zuba mata ido , tace "gwaggo kinajin anti salma" gwaggo tadakatar da ita da hannu "kitashi kawai karki ce komai" mik'ewa tayi tsaye tana ganin jiri tabar gidan.
    Tana fita sukadawo lallashin bingyal "gaskiya mijin nan na raihan akwai bak'ar zuciya ko kunyar dukan k'anwar matarshi baijiba" sume ke wannan zancen.
   Ta dad'e kan ta tayar da motarta kanta kewani bugawa Allah kad'ai yakaita gida lafiya, tanayin parking tafito batareda ta rufe motar ba, a falo tasame shi yatasa gorar ruwa agaba yana kallo, kallo d'aya yayi mata ya kauda kanshi tazo har gurin k'afafun shi tarik'e shi batace komai ba , dakyar ta iya furta kayi hak'uri sekuma ta fashe da kuka yadad'e yana kallonta sannan yace "bansan kinada wannan halin ba ashe yaji yana birgeki kai k'arar mijinki abun burgewa agareki gaskiya kinban mamaki yau naga halinki Wanda bansanki da shi ba" hannu tasa ta toshe mishi baki tana girgiza kai sai kuma ta fad'a jikinshi tana kuka.
     Sun dad'e ahaka sannan yad'agota "yanaji kanki yad'au zafi" kallon shi tacigaba dayi tayi masa alama hannu duk jikinta zafi yake.
"Subhanallah bakida lafiya kenan" yajawo wayar shi yakira faruk yamasa bayani, "OK I'm coming friend".
       Da jakarshi ta aiki yazo domin gwada lafiyar ta, tana kwance a jikin yusuf yana mata sannu kallo d'aya yamata yayi murmushi yajo dab da ita yace "medame kikeji" dakyar tace ciyon kai da zuciya kuma yawuna ba dadi" wata gora yaciro ya bata yakalli yusuf "man ka taimaka mata tayi fitsari asamu ko kad'an zan gwada wani Abu" yusuf yace "mekuma za'ayi da fitasari" faruk yace "tinda dai nace akawo ai seka kawo d'in tukunna".
   Cak ya d'auketa sukaje bedroom d'in ta, gabaki d'aya seda ta amayar da taliyar dataci dakanshi ya gyara ta yacanza mata kaya, faruk yace "sannu fah ciyon naki se hak'uri" yusuf dai baice komaiba ya bashi fitsarin, yajawo PT ( urine test ) ya gwada nan da nan yabada positive.
   Hannu ya mik'awa yusuf "congratulations friend" yusuf yace "for? Faruk yacigaba da rufe jakar shi yace "Alhamdulillah Ashkurki ya rabbi! Yusuf za'a kirani papa baba dad abbu Abba wow Allah abun godiya" yusuf ya mik'e tsaye "karka cemin nanda 8 month kenan agidan nan" "of course friend raihan nada ciki".
     Yusuf ya rungume raihan "thank you so much my wife Allah yasaukeki lafiya" kunya ce ta lullub'eta ta b'oye fuskarta ita kanta farin cikinta baya misaltuwa.
  

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni