FULANIN BIRNI
🎄 FULANIN BIRNI 🎄
© ASISI B. ALEEYU
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
PAGE1⃣2⃣
Har k'asa ya duk'a yagaida ummyn shi ta amsa ba yabo ba fallasa tacigaba da kallonta seda yagaji dan kanshi yace "Umma kince kina nemana".
Volume ta rage tace "Eh dadyn ku yabani sak'o gareka ko ince ya aiko ni in b'ata yawun bakina.
Ya shaida min agaya maka lallai wata d'aya ya baka ka fitar da matar aure yagaji da ganinka a haka".
Gyara zama yayi "amma umma ai shi aure lokaci gareshi idan yazo seka ga har yawuce an manta baya basai ansaka min lokaci ba idan yayi da kaina zan kawo muku suruka har gida".
Mugun kallo ta watsa mishi "sannun ka dai sarkin tsari dayake kaine kahaifemu ba.
Ni zaka gayawa abinda yadace, muyi kaje da kai har uwar dake d'aure maka gindi kuyi abinda kukeso tinda seyanda kuka ce za'ayi sakaran yaro mara tunani".
"Haba umma agabana kike zagin mahaifiyata" baki bud'e takallesa.
"Na zage ta karama mata saboda itace wadda tayi cikinka da shayar da kai katashi kabani guri idan uban naka yazo ka gaya mishi tsare tsarenka"
Jiki ba k'wari yabar mata d'akinta abubuwa sun taru duk sun mishi yawa akai da tunanin raihan zaiji ko kuwa da wannan Sabon shafin.
Laila yahad'u da ita zata kitchen.
"Son kazo ina son magana da kai".
kanshi yadafe oh Allah Matan nan zasu kashe nine daga tsaye , kan doguwar kujera ya kwanta yana jiranta idonshi lumshe yana tunanin raihan.
Yusuf Kodai kafara sonta ne nup yabawa kanshi ansa tana birge nine.
Laila tashigo d'auke da try ta ajiye mishi tazagayo tafara bashi breakfast abaki har ya k'oshi sannan tasa tissue ta goge mishi Baki tabashi ruwa yasha.
Hannun shi takamo tahad'e da nata tana kallon shi shid'inma ita yake kallo yana jiran ta bakinta.
"Yusuf kasani duk duniya banso wani Abu kamar kaiba 'yar da na haifa da cikina takasa samun soyayya irin taka, tin baka san waye kanka ba nake renonka da nuna maka kulawa hakama nake guje b'acin ranka bantaba sonka da sharri ba , nafi kowa sanin waye kai nasan favorite d'inka nasan burinka dan haka nake maka fatar samun ingantacciyar rayuwa mai d'orewa.
Zamanka ahaka bazai yuba duk yanda naso farin cikinka bai kai na mijina da Allah ba.
Dadynka ya takura kanshi yaga aurenka zaman ka ahaka bashida wani amfani kadaure kazabi acikin 'yan matanka d'aya ka kawota gidanku idan anga tarbiyarta yayi dai dai da addini shikenan.
Amma kasani duk wacca zaka kawo bazata kaimun Amira ba sosai nake son had'inku banga abinda amira tarasa ba kake k'inta ina sane da duk abinda kake mata nasaka maka ido ne kurum dan bazan takuraka ba nafi son farin cikinka akan nata.
But zan baka one week kaje kayi tunani akanta duk abinda ka Yanke karka ji komai kazo kasanar dani.
Ido kawai yake binta dashi tinda tafara baice uffan ba , gabad'ai ma yarasa nutsuwar shi metake nufi da duk matar da zai aura bazata so ta kamar amira ba.
Which means kenan bazata so wadda zai kawo ba.
Ni gani banida ra'ayin auren mace biyu nasani bazan iya adalci ba, bana iya b'oye wacca nafi so bazan so Allah yakamani da laifin aikata rashin adalci wa matana ba.
Wani bangare na zuciyar shi yace "karka yi saurin mance halacci karka mayar da son kai akan alkhairi.
Wazan zaba yafad'a ina son raihan she's my type tanada qualities d'inda nake so, yazanyi da Amira.
Wayar shi yajawo yasa kiran faruk, cikin bacci yaji ring d'in wayar shi baitsaya duba wake kiran shi ba kawai yad'aga kiran.
" Faruk I need you right now please kazo dasauri it's urgent ".
"What happened ? Ya tambaya Yusuf yace "nup bazan cen waya bane kawai kazo".
Yana kai nan ya tsinke wayar ya cillata kan kujera ya kwanta kamar maiyin bacci tunani ba Wanda baishigo shiba.
Yazanyi da "yan matan nan biyu ? Anya raihan zata karb'i soyayya ta kuwa?
Zuciyar shi ce tabashi ansa why not kai namijin duniya zaka San yanda zakayi da ita.
Toh amma time d'inda aka d'ibar min bazai isheni ba , bazan so na auri yarinyar da bata sona ba , dole ta koyi sona koyane.
ASEEYAH BASHEER ALEEYU
Comments
Post a Comment