FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE1⃣1⃣

karki kuskura wata k'awar banza tabaki shawarar zuwa gurin wani malamin tsibbu dan a karkato miki da hankalin yusuf.
    ALLAH yafiki Sanin mekike ji idan kika daure inada yak'inin koda baki samu yusuf ba zaki samu Wanda yafi shi alkhairi agareki.
    Amira tak'ara  fashewa da kuka.
"Bansan meyasa nake son shi ba inada masoya Wanda sukafishi komai a duniya iya sanina banida wata matsala da namiji zai k'ini meyasa meyasa" tasake fashewa da wani sabon kuka.

     Raihan tajata suka Shiga mota seda suka hau titi sannan tace mata "inane unguwar ku" gwuiwa low cost tabata amsa.
       Suna tafe tana nuna mata hanya har sukazo gidan , godiya tayiwa raihan sosai raihan tace yiwa kaine.
     "karki manta da karanta hailalala a duk lokacin da ranki yasoma b'aci".
  "Insha Allah zanyi"  bata koma park d'in ba tawuce gidansu.
Abun mamaki tasami motarshi a k'ofar gidansu  bata bi takan shi ba tawuce abunta parking space ta ajiye motar ta.      
      Yafito dasauri yabita amma me koda ya isa tabar gurin "shiiit yafad'a tareda dukan gefen motar shi kiranta yashiga yi amma tak'i d'agawa daga k'arshe ma kashe wayar tayi gaba d'ai.

       Kanshi yadafe wannan yarinyar zata bani headache zanci uwar amira ne rivers yayi yad'auki hanyar g/low cost.
Dai dai wani shago yatsaya yana kallonta yayan ta yarik'o ta sunfito daga wani chemist fuskarta duk ya kumbura yayi ja sosai.
     Dak'yar take iya d'aga idonta saboda azabar datakeji.
    Tsaki yayi yanzu kika fara gani muddin bazaki daina Shiga sabgata ba. Wayarshi yajawo baima San number d'in ta ba yashiga inbox d'inshi yafara dubawa.
Text d'in mata ne birjik dak'yar yagano nata yasaka kira.
    Har ta shiga corridor d'in gidansu taji wayarta na ring gabanta ne ya buga ganin sunan shi a screen.
    Atsorace ta d'aga wayar da wata simple voice nata.
"Gani a k'ofar gidanku ina jiranki" dip yakashe wayar.

      Tafi minti goma tana kallon wayar tajuya ta nufi get can nesa da gidansu ta hangesa adaddafe ta k'arasa gurin.
     Yana ganinta ya bude ganbun mota , bamusu tashiga nan ko ya fizgi motar yafara gudu sosai da yake area ba mutane sosai seda yayi nisa da gidansu sannan ya tsaya yana kallonta.
"Mekika cewa raihan ne? Shiru tamishi tana zubda hawaye.
Tsawa yadaka mata seda motar ta amsa.
     "Badake nake magana ba" nanma shirun tayi ya fizgo wuyanta idonsu sark'e da juna.
     "Kisani bantaba sonki ba hasalima ko birgeni bakyayi natsane manners d'inki ina raga miki ne saboda darajar Ammaty".

      "kifita idona in bahaka ba zakiyi nadamar zuwanki duniya ana so dole ne koya raihan nake so ita zan aura that's all".   
       Yana kai nan yabud'e mota ya hank'adata tareda tada mata k'ura , kukan ma k'in zuwar mata yayi tana tausayin kanta da rarrafe ta isa gidansu bakowa gurin tasamu tawuce d'akinta tafad'a kan gado.
     Kanta ke bala'in Sara har bata son d'aga idonta sama, pillow tajawo ta rungume maganganun shi namata yawo a kai.

       Mutum uku basu samu bacci ba Yusuf raihan Amira kowanne danashi sake'sak'en zuci , yanda yaga dare haka safiya ta riskeshi a zaune.
    Usaina ce tashigo d'akinshi da sallama , ya amsa yana binta da kallon tambaya "yaya barka da asuba umma tace idan katashi tana nemanka ankira wayarka akashe".
     Ko tab baice da ita ba bata damu ba dan tasan halin yayan nata ta juya tabar mishi gurin.
Seda yayi wanka yashriya cikin wani vowel purple bai saka hula ba sai wasu mayun takalmi da agogi k'irar rolex yayi styling hair d'inshi ya zuba turaren diamond dawasu kalan k'amshi yafita.
   " wow bro kagan ka kuwa gaskiya thousands girls they will die".
harara yabita da ita  "sa'an wasanki ne  ni"
    Girgiza mishi kai tayi tana dariya ciki ciki.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI