FULANIN BIRNI
🎄 FULANIN BIRNI 🎄
© ASISI B. ALEEYU
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
PAGE 2⃣5⃣
Basu bari gwaggo ta gane komai ba sun mata bayanin yanda aka karb'e su, taji dad'i sosai tak'ara da addu'ar Allah yak'ara had'a kansu da dangin mijin na raihan.
Raihan ta d'au zafi sosai hakama Yusuf kowannen su yashare wani acewar su an musu laifi dole abasu hak'uri, Raihan kuwa bata da wannan lokacin ko ince bata da wannan tinanin na bashi hak'uri.
Faruk ne yagano da akwai abunda kedamun sa yasa shi agaba dole seda ya mishi bayanin komai, yasauke ajiyar zuciya "gaskiya man kowaccen su tayi kuskure"
Firstly bai kamata amma laila tayi wannan furucin agaban raihan ba domin kamar tafito k'arara ne ta nuna batayi da ita.
Secondly bai dace raihan tayi saurin nuna fushin ta agaban amma laila ba kodan kasan cewarta uwa agareka.
Thirdly kuma Kaine yakamata ka lallashe raihan cikin sigar yaudara daka kware da ita zaka nuna mata darajar laila agunka sekaga ta baka hak'uri, sufa mata seda haka, yanzu dubi wannan abun da sukayi da amma laila d'in 'yar shekara 40 ko fiye da raihan 'yar 27 duk hankalin su yazama d'aya, dole zaka fahimtar dasu kakuma jawa kowacce kunne baka son hakan tasake faruwa.
"Me akayi wa 'yata ne tabbas tayi fushi tinda ko sallama bamuyi ba tiraren dana ajiye mata bansamu na bata ba, shi yasa kake min wasan b'uya dan kar na tambiyeka"
Gabad'an su suka juyo suna kallon ta ummy ce fuskarta ba alamar wasa.
Yusuf ne yayi k'arfin halin cewa "bafa abunda aka mata Kawai halinsune na mata" ta k'araso har cikin d'akin tana hararar shi "kiramun ita a wayarka" shiru yayi yarasa abun cewa.
"Bada kai nake magana ba"
"Uhnn um am ummy ni gaskiya" bata bari ya k'arasa ba ta K'arashe mishi zancen "kai gaskiya bazaka kirata ba"
"No wlh ba haka nake bufi ba zan kirata yanzu" dasauri yasa kiran Raihan amma har sau Biyar bata d'aga ba ya dube ummy "kinga fah sau biyar ina kira tak'i receiving"
Ummy ta b'ata fuska yaushe zata d'aga kiran bayan kab'ata mata rai tin kan tazo family d'in ka zaka fara nuna mata cewa danginka sune kan gaba, ina umurtar ka dakayi gaggawar zuwa gurinta kabata hak'uri sannan kabani ita awaya domin in tabbatar ta hak'ura , wannan umarni ne" daga nan tabar d'akin nashi.
Ajiyar zuciya suka sauke atare , faruk yace "dama ummy na shigowa d'akin ka? Yusuf yace "ba kasafai ba seda babban dalili"
Faruk yayi murmushi "naji dad'in 'yanda ummy ta nuna k'aunar ta ga raihan hakan yafi akan ta nuna rashin so, sedai yusuf nagan kamar ummy ta fara kishin ka agun amma laila"
Yusuf yace "hakane lokaci dayawa Ina mamakin ta bayan itace ta salla mamata ni a yanzu kuma tana Neman kwacewa" faruk yayi dariya "dama wazai iya kyautar d'a haka nan musamman irinka daka zamo tilo agaresu, yanzu dai sai kashirya in rakaka gurin Raihan.
Ba b'ata lokaci suka shirya kasancewar yau jumu'a sai sukayi shigar jallabiya fara tamkar larabawa sunyi kyau kamar asace su agudu bayan anyi sallah suka nufi gidan su Raihan.
Abdul ne yamusu jagora zuwa ciki bayan yarako family doctor d'in su, yusuf yace "waye ba lafiya? Abdul yayi murmushi "raihan ce"
Kai Haba yaushe meyake damunta hup da sauk'i"
Abdul ya kyalkyale da dariya "yi ahankali karka kware wannan abun, bawani Abu bane headache ne Kawai auta ce ke zazzabi harda drip aka samata" huuuu yasauke ajiyar zuciya.
Raihan d'in suka fara dubowa tana kwance ta lullub'e tasaka kyalle ta d'aure kanta.
Har gabanta yaje yadafa kanta fuskarshi d'auke da damuwa.
A hankali ta soma bud'e idonta da sukayi jajir ta saukesu kan shi, yayi mata murmushi "Sannu baby na bansan bakida lafiya ba" itama murmushin ta mayar mishi ta nuna mishi kan gado daya zauna ya girgiza mata kai "nan ma ya isa"
K'ok'arin tashi take zaune yataimaka mata tareda saka mata filo bayanta , se a lokacin faruk yasamu damar yimata sannu kai Kawai ta girgiza mishi, don bata son magana idonta arufe.
Yusuf yacewa Abdul meyasa baza'a kaita hospital ba" Abdul yace "karka damu tasaba yin irin wannan ciyon kan, gaba d'ayanmu munada shi gadon shi mukayi gurin Abba, duk binciken da ake bai nuna cewa wani cute ne ko makamancin hakan ba"
Tausayinta yakama yusuf haka sukaje gun bingyal dake fama da zazzabi se nishi take tana juyi jikinta kuwa kamar wuta, sunyi mata sannu gwaggo na gefenta tana fama da ita suka gaisa da ita kana suka koma gun Raihan lokacin har tayi bacci.
ASEEYAH BASHEER ALEEYU
Comments
Post a Comment