FULANIN BIRNI
🎄 FULANIN BIRNI 🎄
© ASISI B. ALEEYU
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
PAGE 2⃣0⃣
Da murna Yusuf yabar gidan yana dariyar mugunta aranshi yace sai ni yusufah namijin duniya na raihanatu bintu Adam ya kyalkyale da dariya , gaskiya Yusuf bashida tausayi Amira tabani tausayi sosai but shi ko ajikin shi sai ma murnar yake yaci nasara a kanta.
Faruk ya dubesa "anya man akwai zuciya a k'irjinka anya Kanada imani waima kacika cikakken musulmi kuwa" Yusuf ya shure shi "ya isheka ba musulmi bane kafurine original not photo Sat copy"
Faruk yace "koma me zakace wlh bakayiwa yarinyar nan adalci ba ko kunya ma bakaji ba dukda shawarata ce amma yakamata ka lallasheta shine zaka had'a mata harda kiss bayan kasan yana k'ara affection" ka fad'a ya daga itace first kiss d'ina koya tadauke shi ruwanta banda wani case da ita from now, gata nayi mata akan na aure ta bana sonta gwara hakan.
Haka suka cigaba da cece kuce har faruk ya fusata yabar mishi gidan.
Kamar a mafarki Raihan kejin zancen wai an biya sadakinta da Yusuf, tayi dariya ina ma wannan bazai yuba sedai ko kuskure akayi daga gidansu Amira zuwa namu gidan.
Ba b'ata lokaci taciro wayarta k'irar Samsung galaxy s5 ta kirashi, har zata tsinke ya d'aga da murya mai alamar bacci.
"Amaryata yane" ran Raihan ya b'aci tace "amaryar waya? Ya bata amsa da cewa "amaryata man ko baki so kikasance amaryata" Raihan ta bud'e baki tamkar tana ganin shi "Yusuf yaushe muka fara wannan da kai, ina cemin kayi da Amira za'amuku baiko sai kuma naji wani zancen" Yusuf ya kyalkyake da dariya "baby zancen me kikaji? Raihan ta fusata ta tsinke wayarta.
Bai damu ba don ya shirya fuskantar wannan agunta, wanka kawai yayi ya shirya cikin k'ananun kaya M&H rigar yellow wando white yayi styling gashin kanshi ya fesa tiraruka , yasaka glasses blue wow he look damm, babies kungan shi kuwa ya had'u k'arshen had'uwa.
Ya nufi d'a kin ummyn shi ya gaida ita, yanzu wani shiri suke kamar dai kar afiddo zancen auren shi da Raihan, "ummy zanje gurin raihan mezaki bata" ummy tayi murmushi "yaushe zaka kawo mun ita? Ya d'an Sosa k'eya saina shawo kan umma laila" ummy ta tab'e baki tsakaninku , ina zuwa tashiga d'akin ta d'auko mishi Leda "ungo wannan idan kaje ka kira mun ita mugaisa" dad'i sosai yaka mashi yayita zuba mata godiya.
Direct d'akin laila ya wuce 'yar hutu sai hutawa take dama ita ba aiki take ba Sam jikinta na hutu ne, wayaga buzu a kitchen dama fah buzaye haka suke badai son hutu ba, kan k'afafunta yaje ya duk'a tasauke k'afarta tana murmushi ta shafa kanshi "yadai d'ana Ina zakaje? Ya d'an Sosa k'eya, tayi dariya gurin sirikata zakaje koh"
Ya d'ago kai dama "ina son inzo inbaki hak'uri akan abunda nayi Dan Allah kiyafemin ki d'auki raihan tamkar ni tamkar Amira tinda nine nakawo ta" shhhh ta katse shi bakomai haka Allah yaso Amira ba matar ka bace Allah yasanya alkhairi ka gaida mun ita"
Haka yabar gidan su rayuwar shi fes yanaji aransa bashida wata matsala arayuwa, k'ofar gidansu yayi parking yashiga suka gaisa da maigadi yatura shi yaje yagayawa gwaggo da Raihan Yusuf ne.
Bai dad'e ba yadawo yace ance yashigo ciki, bai b'ata lokaci ba ya wuce gwaggo yatarar kan sofa bingyal na kan k'afarta ana sosa mata kai, ya rak'wafa ya gaida gwaggo ta amsa mishi fuska sake.
"Yusuf Kaine kawani tsayawa awaje ay daka shigo Kawai, tinda anzama d'aya"
Ya yayi 'yar dariya "a'a gwaggo shari'a batace haka ba, ya kamata in nemi izini kodan kasancewar akwai mata nan gidan tayu nasame musu a wata shigar, idan aka sab'a shari'a shaid'an zai iya cin galaba akan Mu"
Gwaggo ta gyada kai alamar gamasuwa "hakane kafini gaskiya, Allah yamana jagora" ta zunguri bingyal
"kee bakigan yayanki ba bazaki gayarda shi ba" bingyal ta tunzure baki nifa ban San shiba" gwaggo ta bud'e baki "aww Dama se kin San shi zaki gayar dashi" bata k'ara magana ba ta juya fuskarta gefe , gwaggo ta tashi ni zan shiga ciki kekuma maza kije ki kawo mishi ruwa a kitchen"
K'afa ta bubbuga "nikam gwaggo dik ina masu aikin nan ne seni, bata kula taba ta wuce sama, cike da haushi taje kitchen ta d'auko wani glass cup tareda ruwan faro tazo ta ajiye mishi, haushinta yacika shi ganin abunda take.
"Kee ya tsayar da ita dan ance ki kawo min ruwa shine zaki kawo min zallar ruwa dan kin rainan hankali" bingyal tajiuyo "Ooo Kace yunwa ka ebo yafi wannan kwana kwanar seka jira idan wacca zaka aura tazo takawo maka dan ba 'yar aciki CE ni ba"
ASEEYAH BASHEER ALEEYU
Comments
Post a Comment