FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

®NAGARTA WRITERS          ASSOCIATION

PAGE 1⃣3⃣

Faruk yadafa shi " calm down friend ina da tabbacin komai zaizo yanda akeso"
yusuf da jinsa kawai yake yi yace
   "how kaji me wannan tace bazata so duk matar da zan aura ba inba Amira bace, wannan ai shi ake kira selfishness"
faruk ya furzar da iska yace
    "akwai mafita guda biyu dole kayi d'aya ka jefar da d'aya ita kad'aice hanya mafi sauki agareka"
Yusuf dake binshi da harara yace...
   "c mon kanada shawara amma ka tsaya wani iskanci"
faruk ya k'yalky'ale da dariya.
     "naji kome kace ba laifinka bane soyayya ce.
yusuf ya kaimishi naushi dasauri faruk ya goce yana dariya.
      "kagane friend the only solution shine, kodai ka auri Amira ka yafe soyayyar raihan .
    kokuma kanemi amincewar Amira akan auren raihan,
Ina nufin kanemi Amira su sasanta Kansu da raihan, ta nuna mata cewa ta yafe mata kai .
    I know zata iya yimaka wannan tinda tana son ka, but ni aganina auren Amira shine mafi ah alah agareka saboda tana son ka zata maka biyayya.   
     Raihan kuwa bata ma San kana sonta ba in fact ma zaka sha wuya gurin shawo kanta saboda tana supporting Amira sasai,
 
Yusuf yace..
     " wace irin maganar banza ce wannan , kana nufin sena nemi yardar Amira akan wacca nake son aure" ,
      Faruk ya gutsiri Apple yace .
      " alright sai kayi number one d'in ka auri Amira kowa ma yahuta, cause banga abunda Raihan zata nunawa Amira ba, in fillo da kyau buzu ma bature ne.
   Yusuf kam ya fusata sosai inda abunda yatsana bai wuce auren Amira ba, toh kuma yazaiyi gaskiyar faruk ne zaisha wahala kan ya shawo kan Raihan.

Raihan , surayya da bingyal.
   zaune suke a center carpet suna pepper game   wayar Raihan ce tashiga ruri bata kula wayar ba seda ta bud'e takardun data d'auka , sannan ta lek'a wayar da tsaki tadawo ganin mai kiran , suka cigaba da game d'insu tamkar 'yan primary bingyal cike da farin cikin tafi kowa marking acikinsu.
    message yashigo wayar atare kusan ukku dole ta tsayar da game d'in ta bud'e wayar sak'on farko akace....
    "Amin cin Allah yatabbata ga jinina 'yar uwata fillo dafatar mamana da abbana suna lafiya "
  Sak'o nabiyu....
       " yan matan Yusuf yakike ina Neman afuwa idan nab'atawa sarauniyar kyau da haiba rai , hup my apologizes will be accepted ,
    Sak'on k'arshe...
       " gani a k'ofar gidanku nazo gaida mamana ba gurinki Nazo ba".
Dariya tayi afili ta furta "you're funny" bingyal ta kalli surayya suka kwashe da dariya , take Raihan ta had'e fuska kowaccensu tadaina kallonta .
    " salma kije kishigo da bak'ona acikin gida", sume ta ware ido.      
   "wannan bak'on kodai shine baban babies, wannan ziyara haka times two a week d'aya"
Raihan ta kaimata dundu "to  uwar gulma gwaggo yazo gaidawa his only a friend fah. "
Murmushi kawai sume tayi ta mik'e tsaye  "Allah yakaimu watan biki sis wannan guy d'in da gaske yake kece dai kika kasa gano hanyar shi.
    Bingyal dai anshirya cikin wata siky and blue d'in atampa tayafa mayafi tayi rolling face dashi , tad'auko phone d'inta tana game har ta isa bakin gate.
     "Assalamu Alaika"
Kamar saukar arad'u yaji voice d'inta ya rufe ido yasake bud'ewa , yad'au few minute sannan yajuyo alokacin ta duk'ufa akan game d'inta .
       "Ina yayar taki" yaje fo mata tambaya , kanta a k'asa bata d'ago ba tace mishi.
  "tana gurin koyon sallama da mayar da amincin Allah".
     Leb'en shi na k'asa ya cije wannan yarinyar tagama rainani , dukkan rahmar fuskar shi ta kau yace mata.
     "Up you're terribly face and look in to my eye's"
   Terribly face ta maimaita.
  "of course don't dare cheat you're self kiyi tunanin ko you're beauty , you look like gorilla very ugly face. 
      "wow that's so hot I like you're stylishness it's amizing , zan rubuta ka a dairy d'ina saboda ka taimaka min Nagano cewa inada kyan dayake rud'a samari ciki harda saurayin sister na ta k'arashe zancen da harara idan kagama tsayuwa zaka iya wucewa ciki .

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI