FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 1⃣6⃣

Mr yusuf S/market.
Zaune yake tareda faruk suna lissafin kud'in su atace riba afitarda uwar, faruk ne yaketa murmushi ganin sun samu cigaba sosai yakalli Yusuf yace "Man guys d'in nan fah suna kawo light.
    Yusuf ya gyad'a Kai yana cigaba da typing a computer baya son magana kar ya rikece.
     Siririyar mace k'irar coca cola tazo gaban Yusuf tana yanga cikin wata shiga maras kyau da ita da 'yar arna dik d'aya.
    Faruk kanshi tabashi haushi irin yanda take wani bouncing agaban workers d'in market.
    Kujera tajawo tama kanta guri , ogan ko d'ago kanshi baiyi ba , tasamu damar ce mishi Yusuf kabir binji.

    "Yes Ina jinki"
Ya bata amsa.
Ta d'an tabe baki tak'ara tauna gum d'inta tace gurinka nazo da buk'ata.
    "Sai kin fad'a"
Amsar kenan daya bata.
Tace number d'in ka nake so.
Ya kalleta da wutsiyar ido yace "dalili ko hujja"
   Haba Yusuf kamar dai ba d'an gari ba, number d'in ka ai ba saida dalili ba.
    "Good kije idan kinsamo dalilin kyazo ki karb'a make sure kinada k'wak'k'waran dalili, karki ce uffan kifita daga nan yanzu yanzu.
    Haba Yusuf ta tashi tsaye zuwa gabanshi ta d'an shafo gefen fuskar shi , a harzuk'e yayi jifa da computer dake hannun shi ya kama hannunta yayi baya dashi ji kake rak'a k'as alamun ya mata targad'e  kenan.
     Ihu ta buga sosai Wanda yadawo da hankalin duk masu aiki da masu siyen kaya agurin kanta, Yusuf kuwa tsallaketa yayi yawuce abinshi whiteout saying anything.
  
      Faruk ne yaje gurinta ya taimaka mata ta tashi zaune , saboda matsewar kayan jikinta.
"Kuma Matan nan rawar Kaine da Ku yazakiga mutum ko workers d'in shi baya sakewa kije zuwa mishi wani iskanci next time karyeki zaiyi in baki yi hankali ba"
     Harara ta gallawa faruk "ina ruwanka da kinin bibi" faruk ya shureta da k'afa "ni zaki cewa kinibibi dan na taimaka miki banza kawai marar tarbiya.
   Haka ta kwashi jiki da kunya ta bar gurin , mutane da yawa suna Allah wadai da halinta, wasu kuma suna haushin rashin tausayi irin na Yusuf da wulakancin shi , ganin ba yau yasaba yiwa mata wannan abun ba.
Tareda da dad d'in shi yashigo gidan suna fira da raha tamkar k'awayen juna, suka zauna falo suna cigaba da hirar su, ummy ce tafito sanye da atamfa super tayi kyau sosai kamar bazata haifi Yusuf ba, tagaida mai gidanta da girmama wa.

      Yusuf ya rank'wafa ya gaida ita.
"ummy barka da fitowa"
"Yauwa"
Shine kawai amsar data bashi ta zauna kan d'ayar kujera.
Usaina tayi sallama tadawo daga bikin k'awarta, Yusuf yakirata kee zo nan, gurin ummynta ta tsaya sanin halin yayan nasu.
Ya murtuk'e fuska "waye na ganki da shi dazu"
   Ta dubi ummy ta dubi dad dukansu ita suke kallo.
Yaya salman ne"
"Waye shi?
"Saurayina ne"
Bakinta ya buge "bakida kunya agaban iyayenki kike fad'an saurayi , bari kiji karna k'ara ganinki dashi" ta d'ago idonta cikeda k'walla.
Yaya ina sonshi fah"
"Ki mutu akan shi"
   
     Ummy tace da ita tashi kiwuce ciki, bayan tahaye sama ummy takallesa "meyasa zaka rabata da shi?
Ummy yaron bashida kirki da tarbiya kamar yanda akeso iyayen shi sun sakar mishi kud'i gata yake sha fiyeda zatonku.
    Dad yayi gyaran murya "ka tabbata hakane?
"Yes dad bincike nayi sosai akan shi tin ba yauba seda na tabbatar sannan na mata magana, dakaina nayi binciken shi basaka wa nayi aka mun ba.
    "Shikenan Allah yatabbatar da alkhairi.
Fatar dai mahaifiyar ka ta isar mun da sak'ona agareka.
   Yad'an sosa k'eya.
"Eh dad ta gaya min sedai kwanakin da aka d'ibar min ne sukayi kad'an, amma fah nasamu mata kuma nasan zakuyi alfahari da ita sosai Fulani ce ta usuli basa hausa gidansu".
  Dad ya washe baki "haba dai son Kace mafarkina zai tabbata yar waye?
   Yusuf yace "bansan baban taba amma naji tana bearing Raihan Adam kebi"
   "Aww son Kace yar aminina ka d'auko mun bamuda labari gaskiya zanyi alfahari da wannan had'in"
   Ummy kanta dad'i yacikata har ranta taji son Raihan tin kan taganta.
   Laila da ke lab'e tana jinsu tace "bazai yuba Sam wlh fulanin tsiyar me usuli aka fimu ne wannan zancen banza ne Yusuf bazaka tozartani a dangin muba.



ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI