FULANIN BIRNI
🎄 FULANIN BIRNI🎄
© ASISI B. ALEEYU
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
PAGE 1⃣9⃣
Alh kabir da Alh Adam sun had'u sun tattauna akan zancen auren 'yayan su sosai suka samu mafita , baza ka iya tantance waye yafi nuna farin cikinsa acikinsu ba , sun tsaida rana nanda sati d'aya za'a turo magabatan Yusuf domin Neman auren ta, da haka suka rabu.
Raihan agaban dad d'in ta yana tambayar ta ko kinsan wani yaro Yusuf, tayi dariya "ehh dad ay he's my friend na San shi da dad'ewa" dad yace baida wata matsala koh?
"Kai gaskiya bayada dad ina ma duk macen da zata aure shi murnan samun miji abun kwatance irin shi" dad yace "shikenan tashi kiyi tafiyar ki"
Bata kawo komai ba atunanin ta zuwan dayake gidan su ne yasa dad yake tambayar waye, tana shiga d'akin ta takirashi a waya times two bai d'aga ba taji haushi tayi jifa da wayar tacigaba da sha'anin ta.
Dad yatara matansa biyu laila da Aisha yamusu baya nin halin da ake ciki.
"Matsayina na uban Yusuf kuma wanda Allah yad'orawa hak'k'inshi na aure na ganin na zab'o mishi mace ta gari, na yanke shawara da abokina bayan Yusuf yanuna ra'ayinshi ga yarinyar Adamu ard'o mun yanke zamu had'asu aure kuma batareda wani dogon lokaci ba naga yaka mata kusani mussaman ke laila, biki ne za'ayi na d'an gata biki na gani na fad'a bikin babban d'ana na farko.
Laila taja gauron nunfashi "kana nufin Yusuf bazai auri Amira ba kenan"
Ban hanasa auren Amira ba sedai matsalar daga gareshi take bai nuna ra'ayinsa gareta ba kin sani kuma bazan mishi dole ba"
Bakomai ta fad'a Allah yasa hakan shiyafi alkhairi, ummyn twins bakice komai ba, ummy ta gyara zama mazan ce kungama magana Kace uwarshi kin k'are zance tinda kikayi addu'a Allah yakaimu lokacin.
Ba haka taso ba , ason ranta ummy tayi magana akan Amira sedai taga ta nuna rashin kulawar ta akan hakan, taji zafi ba kad'an ba tadai danne damuwarta ne , amma sosai take son auren Amira da Yusuf gashi ita ka d'ai takewa fatan mallakar shi.
Alh kabir ya gayyato dangin shi na k'auye mutum biyar se aminan shi su ukku akaje zancen auren Raihan.
Shima Alh Adam yatara nashi dangi, anci ansha cimakar Fulani , sannan aka fara gabatar da kai , anbiya sadaki dubu hamsin tareda alawa aka saka wata biyu masu zuwa , acewar su angon yace baya buk'atar dogon lokaci.
"MUHAD'U A KOKO ROAD OPP AA RAJI SCHOOL"
K'arshen text d'in kenan jikinta se b'ari yake anya kau Yusuf ba kuskure yayi ba, ko dai wata zai turawa, kiranshi tayi bugu d'aya ya d'auka. "yade"
Tafara in in yayi saurin katseta "ba mafarki kike ba nine na turo miki message karki b'atan lokaci"
Shiru tayi seda yace "kina jina" da sauri tace "eh gani nan zuwa"
"OK good girl" amsar daya bata kenan.
Ta dad'e tana wanka sannan ta d'au dogon lokaci tana zuba kalolin tirare ba inda baya fitarda k'amshi ajikinta, sannan ta shiga zaben kayan da zata saka duk seda ta hargitsa kayanta dakyar ta fiddo wani swiz less d'inkin riga da skirt yayi matuk'ar karb'arta, light make up tayi ta gyara gashinta tayi d'aurin maryam tad'auko jaka da takalmi da gyalensu set d'aya kalar les d'in ita kanta tasan tahad'u yau ko waye ya ganta dole ya girgiza.
Taja motarta k'arama wadda ta k'ara fito da ita Amira kenan buzuwa mai kyaun zati, dai_dai wani shagon sayarda hijjabai tayi parking tana k'ok'arin gyara parking d'in ta , ta hangoshi shima gayen ba dai had'uwa ba, atare suka fito ya nuna mata kujera ta zauna , dik inda jikinta yake b'ari yake ganin yanda yasha murr.
Ya kalleta yakauda kanshi gefe.
"Bawasa ta kawo ni ba bakuma shawara nazo nema agurinki ba, ke kanki kinsan babban abune kawai zai iya sani nemanki har Mu k'eban ce"
"Ina son ki sadaukarwa Raihan soyayyar da kike min ina nufin kigaya mata cewa kin yafe mata ni hakan ne kawai sai sa takarb'i soyayya ta"
Wani irin zazzafan gumi yashiga ketowa Amira lokaci guda tasaki dariya da kuka atare, kallonta kawai yake bawai tabashi tausayi bane.
"Lallai Yusuf kayi k'ok'ari kai namijin duniya ne, zan sadaukar mata da soyayyar ka Indai hakan zai saka farin ciki zankuma yafe mata kai ak'arshe zanyi nisa daku har sai natabbatar narasaka , Raihan tasameka sannan zan dawo"
Good girl yafad'a kin burgeni kad'an yanda kikayi saurin ganewa wannan ne lokaci nafarko dakika soma birgine" murmushi tayi Wanda yafi kuka ciyo.
"Nima bazan manta wannan ranar ba, ranar da kanemi Abu guna , ranar da nafara birgeka, bazan manta ba gaskiya bazan manta ba" ta k'arashe zancen ta mikewa tsaye "ni zan wuce wish you happy marriage life"
Hannunta yarik'o yakafeta da ido "bata juyo ba sabaoda yanda idonta ke ruwa, shine yajuyo da ita ya tallabo fuskarta , "kin mun kyau da wannan shigar baki taba min kyau ba se yau, kin yarda in baki tukuici ta gyada mishi kai hawaye na bin kuncinta,
Wani personal kiss yabata a lips kafafunta suka d'au rawa tafara tunanin ko mafarki takeyi ne, yak'ara janyota ajikinshi yabata hug tareda bubbuga bayanta alamar rarrashi , lumshe ido tayi inama ace tamutu wannan lokacin cikin wannan farin cikin Sam ta manta cewa bankwana suke da juna.
Manne ajikinsa sun dau Long time seda yatabbatar damuwarta ta kau sannan yad'agota yana murmushi yace "ur sweeter than honey pure with milk" murmushi kawai tayi yajata har mota shine yayi driving d'in ta har gidansu yarakata har d'a kinta kasancewar ba kowa agidan sai ma'aikata kan gado ya ajiyeta yacire mata takalmi ya karb'i gyalenta da bag ya ajiye gefe yaja mata bargo "u have to rest okay" ya bata pk ya mata light off yafita.
Tarasa murna zatayi ko kuka tarasa metake ji bakin cikin rabuwa da Yusuf kokuwa kulawar daya bata wadda bata taba mafarki ba.
ASEEYA BASHEER ALEEYU
Comments
Post a Comment