FULANIN BIRNI

🎄FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 7⃣

Alhaji Adam shine asalin sunan shi daga kebi state.
Kasuwanci yamaida shi sokoto a unguwar sama road , nono yake kawowa a kasuwar gandu sannu a hankali sana'ar ta karb'eshi har yafara shigowa da shanun sa , yana sayarwa sari.
    Kyawon nonon shi yasaka wani babban mai kud'i agadastawa. D'aukar shi aiki yana kula mishi da shanun shi,
     Iya kiyonshi yasaka nonon shanun kyau sosai har suna sarrafashi takowace hanya abun ya bunk'asa yafara yin na kanshi da kanshi , Allah yasawa abun shi albarka ahalin yanzu in kana son yoghurt na k'warai to kasiye Adam yoghurt pure water, ice cream, fura dasauran kayan sanyi sune suka karb'eshi.
   Yanada shop sunfi ak'irga ba abunda basayi har nonon rakumi suna kawowa.
         Malam bubukar shine mahaifinshi.
      Yanada mata d'aya maryama.
Gidansu malamai ne ana koyarwa aciki, Sam basusan wani yare ba sai fulatanci basa hausa ko k'adan.
         Yanada 'yaya shidda Adam ne babba sannan saratu , sai kuma zaruku , khadija , fadimatu , Abdullahi dukansu suna agarin kebi .
Mata uku maza uku duk an aurar dasu, zaruku ma yanada aure harda yara uku marayam mamy, anisa sai jabir, Abdullahi yanada baby daya minal , kowacce bafulatani take aure kuma auren zumunci sukeyi.
      Balaifi sunayin karatu but matan iya junior weac suke aure mazan ne keyin HND , Adam ne kawai yaciga zaman shi sokoto yasamu digree fannin kasuwanci.

        Da kyar iyayen shi da dangi suka yarda yadauki matarshi zuwa sokoto acewar su zai raba kan zumunci seda yamusu alk'awarin zuwa duk k'arshen wata tareda iyalinshi.
      Innawuro sunan matarshi 'yar yayan baffanshi batayi boko ba sam asalin sunanta hauwa'u , zuwansu sokoto ba'a jima ba ta haifi Abdul rahman.
      Yanada yaya d'aya wadda aka haifa kebi sunanta salamatu.
Suna ce mata tunba , iya secondary ta k'are tayi aure a gombe inda take auren dan tsohon sarkin gombe tanada yaya biyu dayar mace tana India gurin karatu namijin yana  Turkey.
Takan jima batazo gida ba.

        Raihan ce ta ukku wadda kebin Abdul suna ce mata sume.
      Sai surayya suna kiranta hari sai auta salma aka maida sunan big sis d'insu itama dai bingyal suke kiranta.
       Fulani kenan dukansu sunyi musu suna bayan sunan yanka , acikinsu ba wadda take haushin sunan da ake kiranta dashi,
     Yaya Abdul soja ne babba , zai kai kusan 31 years Aunty tunba tabashi shekara biyu , sai sume raihan kenan tanada 27 , sai hari surayya tanada 25 sai auta bingyal mai 15 years ,
       Family ne mai cike da soyayyar juna sunada had'in kai sosai , gwaggo suke cewa mahaifiyar su mahaifinsu baffa.
     Sume da hari duk sun k'are skull inda sukayo karatu a saudia , aiki ne kawai basu fara ba , bingyal kuwa tana jss3 .

      Ball suke a tsakar gidan wayar sume tayi k'ara ta kalli bingyal "kidauki wayar".
Da yarensu take fada mata ba musu tad'auki wayar tareda sallama cikakkiya.
     Shiru akayi na d'an wani lokaci sannan tak'ara maimaitawa can cikin mak'ogaron shi yasaki tsaki na tsane sallama awaya ni gashi ban iya amsawa ba.
     Why not kice hey, hello yes, kujimin wannan hekace ba cikakken musulmiba.
    Can yaji tace "Anani koh" Eh "anani" yabata amsa harara tayi kamar tana ganinshi.
A fulatanci take cemasa "dama kanaji bazaka amsa sallama ba ni bazan magana da kai ba" a take ta tsinke wayar.    
      Sake kira yayi tayi rejecting call d'in daga nan bai k'ara kiraba takoma suka cigaba da ball d'insu.

      Ranshi ya b'aci shi wannan 'yar kauyen zata dizga.
Ya koma gida cike da haushinta.
     Wanka kawai yayi yasake dress cikin black suit da wando red yayi styling hair d'inshi so hot tareda watch hublot da white glasses wow he looks breathtakingly handsome .
IPhone d'inshi yad'auko tareda A3 sai baby Nokia ,
Yabude wata k'aramar drawer yarik'a jawo Key's yana maidawa dak'yar yafidda d'aya yafito dashi .
    Gurin laila yaje tana awata katuwar kujera anamata legs massage , gefe d'aya kuma mata ne dauke da try cike da kayan fruits , suna ganinshi suka watse kamar Kullum dai shigarta baya wuce black lifaya sedai tsadaddu ne daga Sudan.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI