FULANIN BIRNI
🎄 FULANIN BIRNI 🎄
© ASISI B. ALEEYU
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
PAGE 1⃣7⃣
Kwance yake kan katifa yana game da wayar shi faruk ya fad'o kanshi "yane" Yusuf yayi jifa da wayar shi yana haki , tuni faruk ya kyalkyale da dariya.
"Amma dai kai d'an iska ne na bugawa a jarida wannan wani irin iskanci ne zaka fad'o min d'aki ba sallama, sannan kazo kaina kacika d'an iss wlh" faruk yad'auko mishi wayar shi yana mai cigaba da dariya.
Wayar shi ce ta d'au ruri ya duba tareda ware idon shi, ya kalli faruk yasake kallon wayar, faruk yadube sa "kad'aga wayar mana" yad'an shafa sumar shi "I was surprise ne wai Raihan ce ke kirana"
Faruk ya tab'e baki "kana wani surutun har wayar ta tsinke"
Murmushi yayi.
"Ba matsala zan kirata but I'm scared fah"
Faruk yace don me kuma?
"Na gayawa mamanta cewa ina sonta amma ita ban tab'a gaya mata ba kasan yanda take goyon bayan Amira shiyake bani tsoro"
Faruk ya nisa yace "haba man kaine fah mata ke tsoro idan sun ganka suna gudu suna b'uya yau kuma Kaine zaka ji tsoron mace macen ma trip d'in ka"
Uhm kawai yafad'a yasaka kiranta har ta kusa tsinkewa sannan ta d'aga bata ce komai ba, shine yafara magana da cewa.
"Hello My"
"Uhn'n hey"
"How are you and how is your family hope everything is moving fine"
"Yes think so" ta bashi amsa.
"Munyi waya da Amira shine kamun k'arya zaka ce wai ta kirani"
Yayi 'yar dariya "haba dai ni nake k'arya da girma na.
"Toh in ba k'arya ba me kayi?
"Kawai bansan mezan gaya mata ba kin sanni ban iya fira ba ko zaki koya mun.?
Dariya tayi sosai "mezai hana zan koya maka in har zaka rik'a amfani dasu"
"Zanyi amfani dasu fiyeda zatonki kedai ki koya mun kawai"
"Shikenan zamu fara darasi gobe, bye bye" b'ata fuska yayi "haba tin yanzu nifa bangaji da jin cool voice d'inki bah"
'yar k'aramar dariya tayi "Next time" dif ta tsinke wayar, ajiyar zuciya ya sauke tareda juya kwanciyar shi.
Faruk yace "umm Mr love ana ta shan love an manta da ni" da Sauri Yusuf yajuyo ya kalli faruk irin hakane d'in nan yace "wlh kuwa na manta da kai yaushe zan tuna da kai ina tareda Queen, faruk ya dubesa da kyau "kabi a hankali kasan mata ba'a zak'e musu" Yusuf ya gyda kai "hakane but ni nawa tsarin da ban ne just stay and keep watching me" ya k'arashe zancen da dariya.
A cikin bacci yadinga ganin Raihan tana zuwar mishi da baby bayanta kuma wata yarinya they look very familiar tareda yara masu yawa kowacce tana mishi murmushi gefen hagu kuma Amira ce d'auke da nata yaron , yarasa gurin wadda zai fara zuwa kowanne yaron shi yake mik'awa hannu, atake ya yanke shawarar zuwa gurin Raihan wadda itace gefen daman shi.
Ya karb'i yaron kenan yana mishi wasa yaji Alarm d'in wayar shi na tada shi 5:00am sallar asuba yayi wani sharaf da gumi hekace yayi tseren gudu.
Zaune yayi yana tuna mafarkin shi kome yake nufi oho, sai kuma yayi murmushi daya tuno cewa Raihan ce wadda ya zab'a ko acikin mafarkin nasa.
Cike da murna yayi brush yayi wanka ya canza kaya bayan yayi alwala yawuce masallaci, bayan angama sallah yabawa liman rafar 'yen 500 yace arabawa duk Wanda yake a masallacin yana buk'atar addu'a. Jama'a dayawa sunyita saka mishi albarka akayi masa addu'a ta musamman sannan kowa ya watse bayan rana ta soma fitowa.
Gwaggo ma da fara'arta ta tashi bacci taga haske sosai da alkhairi acikin istiharar da tayi amma aranta ta aje bazata gayawa kowa ba har sai satin data d'ebarwa Yusuf yacika.
Raihan kuwa tacigaba da sha'aninta bata San wainar da ake toyawa ba sedai Kullum sukayi waya da Yusuf batada zance sai na Amira yaushe za'ayi baiko ba tareda shakkar komai ba yace mata an kusa nan da two weeks dad'i sosai taji aranta har tana shirin fad'a da Amira na k'in Sanar da ita da wuri.
"Gaskiya Amira baki kyauta min ba ace baikon ki da Yusuf nanda sati biyu ki gagara gaya min sena ke ganin baki d'auke ni k'awar shawara ba dukda k'ok'arin danake miki akanshi"
Amira ta nisa "baiko kuma shine yagaya miki hakan ? Raihan tace da abakin waye zanji inko ba naki da nasa ba" Amira tayi shiru aranta tace kenan Raihan d'in bata San cewa Yusuf na sonta ba kokuwa wani tuggun yake shirin k'ulla mata saboda tasan waye shi.
Raihan tace "yanaji kinyi shiru? Amira ta sauke nunfashi "kawai ina tunanin ne kamar na sanar dake dalilin dayasa kikaji nayi shiru kiyi hak'uri please" Bakomai raihan ta bata amsa nan sukayi sallama zuciyar Amira cikeda waswasi , aranta kuwa ta k'udurta cewa bazata mishi zancen ba koma yane abun zai b'ullo nan gaba da wannan tunanin tayi watsi da zancen.
ASEEYAH BASHEER ALEEYU
Comments
Post a Comment