FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 1⃣5⃣

Gidan prof Isma'il.
Gidane babba Wanda ya amsa sunan shi na gida , gidan professor Isama'il kenan mahaifin Amira , prof d'an asalin jiyar yobe state ne kasuwanci ya maidashi Kaduna da sokoto.
    Anan ya had'u da shamsiyya mahaifiyar Amira, yayar  laila wato matar uban Yusuf kenan.
Shamsiyya mace ce mai mutunci da da'a tanada karamci da sanin meya kamata.
     Sam bata so auren prof ba sedan kwai tsarin mahaifinsu ne auren masu kud'i , biyayya tayi ta aure shi bisa tilas badan ranta ya so ba , Sam bata bari yagane hakan ba yanayin biyayyar datake mishi kamar da can ta soshi bare kuma yanzu anyi shekaru atare har ga rabo yasamu.

    Kwance take kan cinyar maminta tana mata gyaran gashi se mutsu _mutsu take saboda tsawon gashin har kan duwawun ta.
    "Mami Dan Allah kirage min gashin nan wlh yana damuna kinga kona saka mayafi seya fito" mami ta harareta sau nawa zan gaya miki haram ne , mahaifinki ma baya son hakan kinfi kowa sani.
    "Uhm umm  take irin Small baby's d'in nan , yayan ta ne yazo , ya gayarda mami ya kalli Amira yace "autan dad gyaran gashi ake ai dakin je African beauty an miki wash and set zai fi"

   Amira ta d'ago golden eye's nata tace "bruh ina kasan wani wash and set harda su sanin gidan saloon" ya Sosa k'eya yana dariya "am im dama dama" se kuma yayi shiru.
       Gabad'ansu suka saka mishi dariya, tsalle tayi bruh yayi budurwa , ya galla mata harara "ko kunya bakiji ba inaga idirisu driver zamu baki tinda duk yawan samarin ki kince bakya so.
   Sai wancan zakin d'an iska Allah koh mami I so much hate him , idan naga yana yiwa sister iskanci, abun haushin bama ita kad'ai ba karki so kiga yanda mata ke rushing d'in shi, yanada page a fb Mr binji's fans , hakama IG karki so kiga followers d'in shi about 9.something.
    Kar kiso kiga likers d'in shi da masu comments duk yawanci mata ne ko tanz baya musu.

    Amira kishine ya cikata da haushin Kanta idonta yakawo k'walla , yacigaba   "ba laifi gayen akwai iya wanka na mutunci baya swag shine kawai damar abun kuma yanada kirki mata ne kawai baya darajawa.
    Mami tace nidai "ya isa haka wannan cin zarafin kaci naman shi dayawa , nikam yaron yana girma Mani , abun mamaki baifi amira kyau ko kud'i ba hakama ilimi , had'uwar jini ce kun kasa fahimtar hakan.
     Amira tace "yanzu mami zai iya k'in aurena? Maminta tasaka dariya "lallai amira Wanda yayi nisa baya jin kira , miye amfanin b'ata lokacin ki da kike akan shi dakinyo zuciyar mu wlh koda son shi zai kasheki zaki barsa"
     Ki daure kiba Mara d'a kunya kifitarda mijin aure kibar zancen Yusuf d'innan hankalin kowa ya kwanta kiriga shi aure  , mamanki laila ma zata huta da wannan jarabar.
     Shiru bata k'ara magana ba aranta kuwa se cewa tace I can bazan iya babu Yusuf ba rayuwa ba Yusuf tamakar Kifi ne da aka dora kan yashi Sam bazai rayu ba.
     Bayan angama yimata gyaran gashin taje d'akin ta , takira Raihan  sundad'e suna waya sannan Raihan tace mata yusuf yakira ki?
    " Eh yakirani wai na kira ki kinyi missing number na"
    Raihan ta kyalkyale da dariya , "Yusuf bashida kirki ba haka mukayi dashi ba kibarshi kawai zamu San mezamuyi agaba , yauwa kinsan next plan d'ina"
    Amira tace
"A'A sai kin fad'a"
Raihan ta gyara murya.
"Zamuzo gidanku gobe"
Amira ta kai zaune haba dai Yusuf d'inne zaizo gidanmu ai wannan ta tsuniya CE "
     Raihan tace lallai Amira baki San waye ni ba, zan baki mamaki kedai kishirya tarbon mu gobe"
   Uhm kawai tace sukayi sallama da juna ta fad'a duniyar tunani .
   

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI