FULANIN BIRNI
🎄FULANIN BIRNI 🎄
© ASISI B. ALEEYU
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
PAGE9⃣
Wayar shi ce tasoma ring yaduba screen d'in ba name saboda haka suka cigaba da firarsu yaji dad'i sosai raihan batada matsala sai dai tana yawan katse mishi hanzari.
Raihan yakira sunanta tad'ago sexy eye's d'inta yace "zamu iya zama k'awaye? seda ta b'ata fuska sannan tace "eh toh zamu iya but ni fad'a zamu rik'a yi da kai in kana b'atawa Amira ina tausayinta dayawa"
Dariya yasoma "lallai kam zamuyi fad'a dan bata gabana kwatakwata bama itaba kowacce mace ta duniya kece mace tafarko dana fara saurara har naje gurin ta gaskiya ke 'yar baiwa ce" hmm.
"Allah yahad'a mune dan in k'watar wa Amira 'yancin ta in koya maka sonta" .
Aranshi yace dama kin taimaka kin koyawa zuciyarki sona zaifimin sauki akan wata Amira tana kallonshi tace.
"mekake sak'awa aranka ? "bakomai" yabata amsa , anan sukayi exchanging phone numbers sannan sukayi sallama yawuce.
D'akinsu taje tafad'a kan gado tace "funny guy" hari ta kalleta " meyazo yi kuma kozaki sake raka shi party ne? Sume ta girgiza kai.
"Nop ziyara yakawo min" hari tace "toh fah kaddai ya zak'e dayawa" bata k'ara mata magana ba tajawo pillow tashiga bacci abunta.
Zaune suke kowannen su yabada nutsuwar shi ga baffan su gwaggo nada ga gefe tana gyarawa bingyal gashinta.
"Dukanku zakuyi mamakin taraku danayi awannan lokacin Ina son kusan cewa duk wani hak'k'i naku dake kaina na saukar nabaku tarbiya da ilimi both na suturceku na cisheku dai dai iyakata banda wani buri a yanzu daya wuce aurar daku mussaman Ku mata.
Kusani Kullum hannuna agaba yake idan na ganku agida raina yakan baci hakama idan kuka fita banda wani sukuni sai naga dawowar Ku sau daya wa nake bibiyarku sai na tabbatar da inda kukaje.
Kusani cewa duk uba nagari bashida burin dayawuce inganta rayuwar 'yayanshi aure shine gatanku dukiyata bazata taba d'aga darajarku ba hakama bazata taba saka ku zama manya ba se da igiyoyin aure.
Shine kad'ai zai d'aga darajar ku za'a raga muku dan darajar aure za'a muku hidima saboda darajar aure.
Sallar mace mai aure d'aya wadda akayita yadda akace tafi sallar Mara aure goma sai kinyi kwana arba'in kina sallah kafun kisamu ladar sallah daya ta mai aure.
Aljannar mace batada wuya agidan mijinta wutar ta ma batada wuya , girki wannan idan kunsan ladar dake cikinsa bazaku bari wata mace tayiwa mazajenku girki ba.
Kundai ga mahaifiyar ku duk shekarunta bata gaza gurin yimin hidima ba.
Kai Abdul kafara isata ka gota 30 amma ko zancen aure bakayi da kunsan yanda dangi suka dameni akan aurenku da kun fitar da abokan rayuwa , Abdul yace .
"Dan Allah baffa kayi hakuri dama ni gini nake ina son sai nagama sannan in nemi mata Alhamdulillah nakusa k'arasawa yanzu ina kan lefe kabamu nanda sabuwar shekara insha Allah komi zaizo k'arshe".
kowa yamaida idonshi kanshi gwaggo tace.
"yaushe kafara gini da har kagama bamuda labari ? Murmushi yayi.
"Gwaggo kenan kamata inada aiki ina kasuwanci ai yakamata in rik'e kaina ahankali nake ginina shekara biyu yanzu kuma anzo k'arshe.
Sannan nasiyawa raihana da surayya gado da kujeru daga China basu iso bane sauran kayan seku k'arasa" hawayen dad'i suka zowa iyayen atare albarka sosai suke saka mishi.
"Lallai ka nuna min Kaine babba kuma na yarda ko bayan raina zaka rik'e 'yan uwanka Allah shiyimaka albarka".
Rungume shi sukayi suna godiya hug back d'insu yayi , "insha Allah baffa atare zamuyi aure " bingyal tace
"Baffa kyalesu ni nan duk sena rigasu aure" kowannen su yaware ido baffa yace "waye mijinki to" kanta tasanya acinya "addu'a zanyi irin wadda gwaggo kemuna allahuma miji nagari" dundu gwaggo takai mata "Mara kunyar yarinya".
ASEEYAH BASHEER ALEEYU
Comments
Post a Comment