FULANIN BIRNI
🎄 FULANIN BIRNI 🎄
© ASISI B. ALEEYU
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
PAGE 2⃣4⃣
Da murna ta karb'e su tareda musu izinin zama, Yusuf yakoma gun k'afafunta ya zauna yana ta jefawa raihan murmushi, wadda kanta ke k'asa tinda suka shigo, yanuna ta yana dariya.
"Ammaty kinganta can fah sewani kame_kame take, kisaki jiki nan gidanku ne"
Laila tayi dariya "gaskiyane ba banbanci da gidanku, sedai kuma son wannan bata fi Amira nah komai ba , ni nazata wata zuk'ek'iya ce takasa 'yata ashe ma dasaura wannan kuwa tayi karatu naganta k'arama"
Ran Raihan ne yab'aci tace wa , surayya tashi muje gida atare suka mik'e tsaye , Yusuf nata soshe soshen kunya "kubari zuwa anjima muwuce" Raihan tabishi da harara.
"Nida banyi karatu ba yaza'ayi na zauna gun masu karatu kasake tunani" tana kai nan tasakai ta wuce.
Laila ta rufe baki "aww kaddai ni yarinyar nan zata maidawa magana" Yusuf kuwa duk yarasa nutsuwarshi.
"Son badai akan wannan kake ta had'o gumi ba kodai ta asirceka ne bantaba ganin wannan a idonka ba" shiru yayi yarasa abun cewa.
Usaina ce ta taresu kaddai har kun fito anti, Raihan ce ta bata amsa da "kwarai kuwa baikamata marasa karatu irin mu suzaina a irin wannan gidan ba"
Tajawo hannunta "antina meya farune? Sume ce ke bata bayanin yanda akayi, usaina taja tsaki "zata iya tinda dai ank'i auren buzuwar 'yarta shine takewa bak'in ciki, Dan Allah kuyi hak'uri sisters"
"OK dama Amira 'yarta ce? Usaina ta kalli Raihan kin Santa ne?
"yup nasanta sedai bamu dad'e tare ba"
Usaina ta tab'e baki "yar yayar tace shiyasa take jin haushi" dai dai nan Yusuf yafito turus ya tsaya ganin usaina tareda su.
Ya b'alla mata harara "mekike anan" banza ta mishi ta juya abunta.
"Ke zo nan kika sake naji wata magana gurin ummy wlh ranki zai b'aci"
"Toh ni mema zan gaya mata"
Banza yamata ya maida hankalin shi gun Raihan, wadda taja hannun surayya sukayi gaba, abakin mota yasamesu.
"Haba Raihan wannan fah mahaifiyata ce da kike gani meyasa rashin hak'urin ki zai fara fitowa tin kan aje ko ina"
Kallon banza ta bishi da shi "bawani dogon zance Muke soba kazo ka kaimu gida daga nan ka karb'i sadakin ka seka kaiwa 'yarta yar boko mai kyau" hannun shi ya dun k'ule ya bugi mota "meyasa kuke son bani headache ne bana son hayaniya meyasa"
Surayya ce tabashi hak'uri dakyar ya yarda ya kaisu gida, acikin motar ne surayayya ke tambayar Yusuf waye mahaifiyar sa ta gaskiya, "Ammaty man itace uwata ko baki gane ba"
Raihan tayi murmushin dake tattare da haushi tace "Ashe kai buzu ne, banida labari sekuma naga kamar ka da Fulani tafi yawa, garin ya ka iya fulatanci amma bakajin yaren buzaye"
Kallonta Kawai yake yakasa cewa komai tacigaba da cewa "ummy ce mahaifiyar ka ummy ce Fulani jininmu, mahaifiyar ka ce zata kushe abunda kazo dashi kana so, mahaifiyar ka ce zata yi ky'ashin matar da zaka aura agaban ka, bazai yuba ummy uwace, ta k'ara gyara zamanta a mota, ta karb'e mu hannu bibbiyu bata nuna mun komai ba sai zallar soyayya wadda tasamo asali daga soyayyar ka naga k'aunar ka mai tsanani atare da ita.
Naga so mai launi uku atareda ammaty d'in ka ta gauraya soyayyar ka da abubuwa da dama"
K'iyyyyy ya tsayarda mota ya cakumo wuyan raihan sewani huci yake tamkar kumurci "ki zage ummy kigaya mata dik abunda kike so ban hanaki ba amma kisani tab'a Ammaty ko zagin ta agabana had'ari ne bazan jure ba, nayi kuskuren rashin Sanar dake darajarta agurina banda kamar ta aduniya"
Clapping hands ta mishi "good job" sannan ta gimtse fuska sauke ni a motar nan bana buk'atar ganinka a wannan yanayin.
Bai tsaya ba itakuma ta bud'e ganbun motar dasauri ya tsayar da motar ta fita tajawo surayya wadda kanta yad'au zafi.
Ya kife kanshi a motar, tin yanzu zan fara fuskantar k'alubale meyasa su biyun basu fahimci muhimmancin junan su ba meyasa suka kasa gane cewa kowaccen su tanada b'angare a rayuwar shi, bazan butul cewa ammaty ba akan mace, bakuma zan rabu da raihan ba tazama wani sashe na jikina Wanda bazan iya babu ita ba.
ASEEYAH BASHEER ALEEYU
Comments
Post a Comment