FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 2⃣2⃣

Morning text d'in shi ne yatada ita bacci misalin 7 o'clock, da d'an tsaki ta farka taje tayi brush tajawo wayar tana dubawa.
"Fresh flower for you, thinking of you dear now and always, just to say good morning!"
   Tab'e baki tayi tajefar da wayar kan gado ta k'ara komawa baccinta, bata farka ba sai 10 tayi hamdala ga ubangiji sannan tak'ara yin brush tareda wanka tasaka kaya Mara nauyi tasauko k'asa domin karyawa, ita kad'ai ake jira lokacin kowa ya halarta, gaisuwa ta mik'a musu sannan bingyal da sume suka gayarda ita, anutse suke cin abincin su kowanne yazuba abunda yake ra'ayin ci, suka k'are akayi addu'a aka sauko kan carpet.
       Raihan dame_dame kike buk'ata na aurenki? Dad ne yajefo mata wannan tambayar, kanta k'asa tace "dad inaga muje tareda bro Jidda muyo siyayyar gaba dai" Abdul ya kalleta "yaushe kenan auren da aka saka in three month nima fah inada abunyi kinsani"
"Haba dai bruh kasani sarai Abba bazai barni inje nikad'ai ba dole seda babba" gwaggo ta karb'e zancen da cewa mezai hana kijira yayarku kuje tare tinda tace end of this month zata shigo kinga ita mace ce tafishi sanin medame ake buk'ata koya kukace?
      Gabad'ai suka amsa da yayi, bingyal ta shiga tsalle antyna zatazo wayyo dadi Allah yasa hutun su najwa yak'are kan lokacin azo da ita
  Faruk ne tareda Yusuf a Mr Yusuf S/market. Suna tattauna yanda auren zai kasance, Yusuf yace dole fah sena je Malaysia in gayyato manyan friends" faruk yace wannan yawone kurum me ba'ayi yanzu Kawai katura musu IV Wanda yazo toh Wanda baizo ba shikenan" Yusuf ya kurb'a lemu "Ehh wannan shawarar tayi" suna a haka ne Abdul yazo tareda bingyal sunyi matuk'ar kyau kamar shi ya haifeta saboda kamar su.
      Sanye take cikin Riga da wando pink and white ta yafa wani gyale white da glass d'in ta pink wow kungan babyn nan kuwa she look very natural hot, Abdul kuwa komai nashi white ne shima gayen badai kyau ba yasaka irin medical glasses d'in nan, faruk ya zunguri Yusuf ga sirikinka can zuwa, gaskiya yarinyar nan ta had'u Allah yabani baby irinta, dubi d'an small pinky lips d'in ta kamarsu d'aya da Raihan gabadai ma kamarsu d'aya sedai kamar babyn nan zata fisu kyau amma fah setayi iyayi wannan ji yanda take turo baki"

     Yusuf ya bigesa "ay sekaje ka lasheta in banda shashanci miye na tsayawa kallon wannan da ko gama halittarta ba'ayiba" dai dai nan sukazo gurin Abdul yabasu hannu sukayi musabaha , bingyal ta d'an turo baki Wanda yake k'ara mata kyau, ta kalli faruk yaya barka da hutawa ta d'an harare Yusuf sannu tareda b'ata fuska.
   Ko kallon inda take baiyi ba ya cigaba da magana da Abdul, yana gaya mishi next week zai wuce dubai da saudia idan yagama umra zaije Jidda ya had'o lefe , Abdul ya rik'e baki "duk Nigeria bata isheka had'a lefe ba sekace outside" Yusuf yayi dariya "da nikuwa tare zamuje kaima kahad'o naka" Abdul ya gyara zaman glass d'in shi "ba inda zan je wani had'o lefe ina Nigeria, tukunna ni ko mata ban nemaba"
    Guri tasamu ta zauna tana d'aukar selfie da wayar ta, dik abunda take faruk na kallonta se murmushi yake har ga Allah yarinyar ta burgeshi.
      Abdul yacewa Yusuf "shopping zanwa auta zata koma hutu ne" Yusuf ya kalli inda take zaune dai dai inda ta turo baki tana d'aukar hot selfie ta turo baki ta zare ido, gabanshi yayi muguwar fad'uwa saboda yanda tayi kama da raihan har za'a iya kiransu da twins yasake kallon Abdul shima dik kamar ce sedai Abdul da bingyal sunfi kama idonsu yafi girma kamannin sume yazo mishi itama irinsu ce sedai ita chocolate ce.
   "Boarding skull take ne? Abdul yace "no yana dariya khalipha international pri and sec skull take" Yusuf ya mishi nuni da su shiga ciki , nan yaga irin soyayyar da Abdul kemata don kyaleta yayi ta zab'i dik abunda take so tin kan cornflakes, kalolin cake da snacks bired, kiri milk etc , seda tagama nata sannan shima ya zab'a mata, ta d'auki ice cream tana sha suka fito waje.
     Ma'aikatan se kallonsu ake gwanin saha'awa, yabiya kud'i suka wuce gida, faruk ya sauke ajiyar zuciya "lallai anaji da wannan autar kagan yanda yake kashe mata kud'i sewani shagwaba take kamar yar 2, Yusuf ya tab'e baki " kaji dashi ni wlh haushi yarinyar nan kebani" faruk ya harare shi "toh meta maka na haushi"?
    Yusuf ya bashi labarin tin randa suka fara waya da ita har zuwa muguntar da ta mishi a girki, dariya kamar zata kashe faruk yace "no Wonder friend Allah wannan rawar kan nata zata iya halin yayarta ne har ta fita ma amma fah ta birgeni wlh gwanda ta rama in ba haka ba kasamu madaddalar zalinta"

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI