FULANIN BIRNI
🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI. B ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 4⃣0⃣ Muhammad salim shine sunan da aka bawa yaron, sunfi kiranshi da salim se ummy ce ke kiranshi da Muhammad. Daga shi har maman shi suna asibitin ana kula dasu, sosai yusuf yake hak'uri da danne damuwarsa akan zaman asibitin sedai bashida yanda zanyi , a haka sukayi wata d'aya da sati biyu ya dame faruk akan shifa yana buk'atar matarshi dole faruk yabasu sallama suka koma gida. Wata tsohuwa daga binji aka d'auko tana kula da salim tareda nuna wa raihan yanda zatayi wankan jego, kyakkyawar kulawar dasuke samu ta sanya sukayi b'ulb'ul abunsu kamar basuda matsala. Bingyal na matuk'ar son salim yusuf ma yafahim ci hakan saboda haka ne yake d'an d'aga mata k'afa akan rainin wayonta, har yakance tafi raihan sonshi. Lokacin daya cika shekara d'aya Amira tad'awo Nigeria bayan ta kammala degree na biyu, itace ta had'a mish...