Fulanin birni

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 3⃣0⃣

Yusuf
"Gaskiya surayya ta iya had'a girki irin wannan delicious haka anya zan iya driving kuwa" Raihan dai sai dariya take tana mamakin yanda yake ta zubawa cikin shi kamar bashi keci ba, yajawo jug d'in zobo dayaji pineapple yafara kurb'a nanma lumshe ido yayi.
   "Babyna mijin surayya ya huta, but nasan dai kinfita iyawa."
"Umm baby kenan ai a gidan nan kowa ya iya girki bazaka banbanta hannun raihan da surayya ba bare na auta kuma gwaggo bata barinmu bacci semun shiga kitchen everyday."
    "Amma baby ai auta bata iya ko dafa ruwan zafi ba she's too young fah" raihan ta ware ido "tab ga girkinta kana ci harda santi."
   "What ya fad'a tareda maida spoon a plate".

   Raihan tayi dariya "yes itace ta girka surayya na wani aikin har zob'on itace tayi yakaji girkin nata ne."
    Murmushin k'arfin hali yayi "um ba laifi yayi dad'i sedai yaji ne yasoma yawa aciki".
     da gudu take saukowa downstairs rik'e da Teddy bear d'in ta tana dariya da alama ta tsokano wani ne, cak ta tsaya ganin mutum agabanta yawani zama yana cin abunci, ta kalli raihan ta b'ata fuska.
   "Am sis dama wannan zan wa girki kikace inmiki kan kidawo? Raihan tace "ehh shi ne da wani abun ne.?
   "No ba komai."
"Zan sha bak'in shayi." Muryar shi ta tsayar da ita , kamar bata jiba yace "Salamatu dake nake" wayyo zokuga haushi, raihan ta zaro ido "baby kajawo mana rigima bata son ana kiran ta salamatu." Kafad'a yad'aga irin ko ajikinsa d'in nan.
    "Wallahi bazan dafa ba ni zaka aura daza'a rik'a sakawa aiki ga matarka agabanka."
    Fauuu Fauuu kakeji raihan ta wanketa da mari "yaushe kika aro wannan halayen na rashin kunya da rashin mutunci , yusuf sa'anki ne, da Abdul ne zaki gaya mishi haka."
   Dafe da fuska take kallon 'yar uwar tata "sister yau ni kika mara saboda miji."
   Raihan tayi saurin katseta da "karki k'ara magana je ki dafo min black tea" ba musu ta juya taje ta had'o mishi shayin ta ajiye ta koma d'akinta tana rusar kuka raben da adaketa har bazata iya tunawa ba.
    Yusuf kuwa fad'a yasakawa raihan kan saboda me zata daketa dukan ma se mari , aranshi kuwa yaji dad'in hakan.
     Wunin ranar bata fito waje ba ta kulle kanta d'aki tana kuka har fuskarta ya kumbura tana bak'in cikin dukanta a gabanshi, mirror ta duba tana kallon swelling face d'in ta, dasauri ta jawo tissue ta goge idonta.
     "Wallahi sena maka sharri bada ni kake ba sekayi regretting sanina a duniya."
      Wanka tayi ta sauya kaya tayi sallah sannan ta sauko k'asa, gaba d'ayansu suna a falon wani drama suke kallo a MBC drama.
     Batayiwa kowa magana ba taje kitchen ta had'o ma kanta abunda zata sakawa cikinta, anti tunba tace "auta waya tab'a min kene kiketa fushi" murmushi tayi "bakomai anti banajin dad'i."
"Bakya jin dad'i shine kike kuka tindazu mukayi lunch baki fitoba" surayya ke zancen, bingyal ta kalli gefen da Raihan take wadda itama ita d'in take kallo tace "ehh sis kaina yayi ciyo amma naji sauki" gabad'ayan su sukace Allah yasauwaka.
      Key tasawa k'ofar sannan ta bud'e wata k'aramar wardrobe tasauke dukkan gifts d'in ta, zaune tayi tana warwarewa wasu chocolate ne masu tsada da kyau wasu flower ne mai kyau, haka dai tacigaba da bud'ewa har tazo kan na yusuf kamar ta jefar dashi awaje sekuma ta bud'e anyi rubutu mai kyau happy birthday salsuf, tadad'e tana maimata Kalmar salsuf , ta d'aga kafad'a myb acikin fulatanci ne akwai words masu wuyar gaske aciki.
    Happy birthday honey bear baby dariya tayi sosai wannan gift d'in faruk ne, manyan biscuits ne da sweet masu shegen dad'i.
      Sark'ar  data fado ne tarasa inda tafito styling heart gareta red color favorite color d'in ta kenan, acikin akayi zanen S&S love, "wow" ta fad'a sosai abun yabirgeta se dariya take zoben ma iri d'aya se a lokacin ta lura gold ce "wannan kyautar se big bro Abdul much love for you yayana"
      Tasake bud'e wata leda mezata gani kuwa in ba lizard ba wani irin ihu ta buga tabud'e k'ofa da kyar sannan tahau tsalle a step tana kwala ihu bibbiyu take takewa dakyar tasauka k'asa ta zube sumammiya.
    Dai_dai nan suka fito gwaggo tarabka salati "na Shiga ukku meya same auta" kowannen su da tambaya abakinsa k'ofar d'akinta sukagani abud'e anti tunba da Raihan sukayi d'akin aguje dan ganin meke faruwa.
       K'adangaren roba suka hango sak kamar mai rai yana yawo, suka kalli juna suka maida dubansu gun gifts d'in ta, anti tunba tabuga tsaki "wani jakin ko jakar ne suka mata wannan Sharrin ansan yarinya na tsoron shi shine za'a sako mata shi Allah zai saka miki takwarana.
    Ta dad'e kan ta farfad'o da kuka ta tashi duk ta burkice musu se addu'oi suke tofa mata dakyar akasamu ta nutsu ranar dai dak'in gwaggo ta kwana tsabar tsoro ko k'ofar d'akin ta bata son gani

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI