Fulanin birni

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE2⃣9⃣

Cikin isa da k'asaita irin na laila take jifanshi da mugun kallo, wanda yadad'e baiga irinshi ba, kanshi ak'asa zuciyar shi ta soma bugawa "menayiwa Ammty na take min wannan kallon mai d'auke da tuhuma" muryarta ta katse mishi tunani da cewa "Son kana kokonto akan soyayyar danake maka? meyasa nakasan ce abun b'oye sirri a 'yan kwanakin nan meyasa na zama abun rufe sirri agareka, an kamani da wani laifin kokuwa kagan canji a gurina kodai kanason komawa mahaifiyar Kane lokacin dana gama d'awainiya da kai naci kashinka naci fitsarinka ciyonka yazamo nawa banida wani sukuni matuk'ar bakada k'oshin lafiya."
  
      Yusuf ya d'ago sexy eye's d'in shi yace "Ammaty nayi miki laifi ne kike min gorin kulawa baki tab'a fad'ar haka ba, ammaty bana boy'e miki sirrina sedai ko idan nasan cewa zai iya zama damuwa agareki, nikuma bana son saka ki a damuwa, bana shakku ko kokonto akan soyayyar dakike min ke uwata ce kinada iko akaina bawai kuma na shirya barinki ba saboda ummy dukanku iyaye nane bawani banbanci, kiyanke min hukunci akan laifin da kike zargina akai, sedai ina mai baki hak'uri bana ganganci gurin sab'a umarninki seda kuskure wanda yazamo tilas agun kowani bawa."
    Dogon nunfashi taja "yusuf na yarda da kai karka juyamin baya" hannunta yarik'e "bazan tab'a ba ammaty har k'arshen rayuwata, kifad'i mekike so in miki yanzu" murmushi tayi tareda cizon leb'enta na k'asa.
  
         "Kaje ka kawo min schedule d'in bikinka kazo muje gidanka ingan me ake buk'ata inaso komai yakasance hannuna" ya kafeta da ido anya batayi son kai ba , idan akace komai hannunta toh danginshi fah da mahaifitar shi, murmushi yamata "bakida matsala da wannan kishirya gobe semuje."
      Fatim ta wuce su cikeda haushin su ta haye sama tana gunguni.
    "Keee zo nan yakirata da lion voice d'in shi, cak ta tsaya ba tareda ta motsa ba.
     Laila ta tadaka mata tsawa "Dan ubanki ba kiranki akeba uban me kika tsayawa can harda bawa mutane baya"
     Juyowa tayi ranta b'ace sedai tayi saurin had'iye b'acin ran nata lokacin da sukayi four eye's da shi.
    Ya kalli laila ya kalli fatim "Ammaty kizama shaida wallahi tallahi idan fatim ta k'ara fita bada izinina ba ran kowa a gidan nan seya b'aci, ke idan aure kikeso kifidda mijin auren ay bawani abu bane inkin k'oshi da bokon amma kitabbar na bincike addininki naga bakida 80% aciki wallahi sekin koka bake ba bokon kuma a aurar da ke ga wanda mukaga dama."
  
         Laila ta k'ura mishi ido tajuya gurin fridge ta d'auko mishi ruwa , k'in karb'a yayi seda ta d'an langab'e kai.
   Dadynsu ne ya katse musu tsayuwar da suke, "Me ya faru nake jiyo ihun yusuf tin a waje"? Laila ta gyara zaman mayafinta tace "shida k'anwarshi mara jin magana."
    "Good kasaka ido sosai akan su ni na baka umarni duk wadda tasaba dokar gida da addini kayi maganinta kobayan raina kaine gatansu."
Yusuf ya rankwafar da kai "dad kawai abasu izini duk wacca take da miji ta turo amusu aure ina tsoron yawan tara samari da ayi gwanda ba'ayi ba in karatu zasuyi yazama dole sumaida hankali akanshi arabu da duk wani saurayi , in kuma aure sukeso amusu kan sujawo mana afun fad'e."
   Dad yajuya yana tafiya "wannan gaskiya ne ka tara minsu har iyayensu dasafe zamu tattauna akai."
   
      Wata irin yunwa kedamun sa yamanta raben daya sakawa cikin shi abunci gashi kuma macaroni kawai yakeson ci , yakira Raihan awaya "hello bae kina gida ne."
"Eh but na d'an fita tareda anty salma."
"Yunwa nakeji zaki dad'e ne?
"Umm ba matsala zan kira surayya ta dafa maka nasan dai favorite d'in ka macaroni."
Dariya yayi "yup bae ayi mai kyau in the next 20 minute zanzo inci".
"Bakada matsala mijina sekazo."

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI