Fulanin birni

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 2⃣8⃣

Gwaggo
"Yaka mata aje kebi a d'ebo 'yan uwa masu muhimmanci ayi tsare_tsaren bikin nan dasu."
       Tunba ta girgiza kai tana shan rake, "haka ne gwaggo, amma abari zuwa two weeks haka zanje da kaina tareda amaryar musanadar dasu daga baya se atura driver yad'auko su, inna dije da saratu se inna inno, kinga dukansu sunada wayewa ta yau da kullum a hannunsu kad'ai zaki bar Raihana su gyarata ni zanji da gyaran jikinta.
    Gwaggo tayi murmushi "wannan shawarar tayi lokaci na tafiya duka yau saura kwana nawa" Raihan ta murguda baki "akwai wata d'aya fah ko yanzu sewani zumud'i kuke zan bar muku gida."
    Ga bad'ayan su suka Samata dariya.
Tunba tace "ke in banda abunki ai gata ake miki gidan mijinki kama da mi, ta tab'e baki "gidan ubana ma kama da me yake."
     Sallamar shi ce ta maida hankalinsu gun k'ofa tare yake da usaina da hasana sunyi Shiga kala daya atampa java dinkin niger sunyi matuk'ar kyau, dasauri Raihan taje ta tarbosu tana musu sannu da zuwa.
Sun gayarda kowa a gurin sannan suka zauna, shima ya gayarda gwaggo da tunba yasamu guri ya zauna.
Usaina tayi gyaran murya "antynmu kinganmu ba sanarwa ko"? Raihan tayi murmushi batace komai ba, usaina tacigaba "Dama wani event ne muke son had'awa a bikinku Fulani's day, shine to ummy tace semun sanarda ke dik yanda kikace."
    Raihan ta nisa ta kalli sume da tunba kasancewar gwaggo tabasu guri tin d'azun, gabad'ayansu suka gyad'a mata kai alamar gamsuwa, murmushinta tayi.
       "Bakomai sisters ai da baku wahalda kanku da zuwa nan ba kuma kunada naku 'yancin abikin kusanma kune manya k'annen ango" dad'i sosai yaka masu.
   Yusuf yabisu da kallon tambaya "meyasa kuka mun k'arya" hasana ce tayi k'arfin halin cewa "yaya munsan zaka hanamu ne shiyasa mukayi shawara da ummy kuma ta bada izinin hakan shine tamu guddumawar abikin."
    Harara yabita da ita "nikuma banida ra'ayi Kenan baza'a tambayi nawa ra'ayin ba bare aji menake so akai."
Raihan tace "Oh bae so sorry nida kai ai bakinmu d'aya idan nace eh nasan barakace A'a ba kawai kamusu uzuri bazasu k'ara ba."
     "Saboda kece mijin nice matar ba, shiyasa idan kikace eh bazan ce a'a ba".
"No ba hakaba kawai kayarda ni Ina so" ta kafeshi da ido wanda ke k'ara masa sonta, dasauri ya kawar da idonshi gefe.
     Hasana ta kalli bingyal dake saukowa downstairs tace "wannan ce akayiwa birthday? raihan ta bata amsa da "ehh" bingyal data wuce kitchen ta fito rik'e da robar ruwa hannunta tace "sis bak'i mukayi ne? "Ina wuninku" suka amsa da "lafiya lau" har zata wuce raihan takirata "bakigan yusuf bane"?
"Aww ay ca nake suka d'aine sannu yaya" tawuce abunta , ya rakata da harara aranshi yace 'yar rainin hankali mara tarbiya.
        Haka suka cigaba da  tsare_tsaren bikin har yusuf yagaji yace zai wuce badan sunso ba suka bar gidan, kowannensu yanajin dad'in kasancewa da juna.
     Ball suka taradda bingyal nayi cikin shigarta ta sportswear tanade gashinta guri d'aya kayan red colour tayi kyau, usaina ta kwala mata kira tazo se haki take.
     "Har zaku wuce? ta jefamusu tambaya tana kurb'a ruwan faro, hasana tace "em zamu wuce semunzo d'aukar ki muje gurin had'o decoration na Fulani" usaina ta karb'e zancen da cewa zatayi kyau a presenter koya kuka gani? Bingyal tayi dariya har wani presenting zanyi bayan ga sister surayy."
   Horn ya buga musu dasauri suka bar gun suka wuce tareda yiwa juna sallama.
      Laila ta kirashi da tana nemanshi bayan angama sallar magrib, cikeda girmamawa ya karb'a mata da "senazo insha Allah.''
    Gurin ummynshi yafara zuwa ya mata sannu tana fama da mura irin tasu ta fulani, ummy takirashi da maza sunan datake kiranshi kenan "Baka tsaida ranar wedding meeting d'in ba, yaka mata musan tsarinka musan me zamu gyara me zamu k'ara aciki."
   Yusuf ya gyara zamanshi "ummy narasa wayafi zumud'in wannan bikin tsakanin gidanmu da nasu raihan, narasa wayafi farin cikin auren nan tsakanin iyayena danata" ummy ta tashi daga kwanciya tana kallonshi tace "bawanda yafi wani suma suna murna kamar mu amma bana jin akwai wanda yakaini farinciki da wannan ranar hakama wannan had'in yayi sedai fatan alkhairi da zaman lafiya."
    Yusuf ya matsa daf da ita ummy wannan ne karo na farko dana fara ganin wani abu a idonki saboda ni, ummy ashe kina sona haka, ashe kina farinciki dani ummy kisamun albarka kamar yanda kowacce uwa kesakawa d'an ta."
  Hannun shi ta kamo ta rik'e idonta tab da hawaye, takira sunan shi "yusufah" karo na farko daya fara jin takirashi da sunan shi, "duk duniya babu mai son ka sama dani babu mai k'aunarka kamar mahaifiyarka ashe kana son albarkata. nayi kyautarka lokacin da nafi kowa bukatuwa da kai naraba hanta da jini nazabi farantawa mijina da abokiyar zamana"
Allah yamaka albarka yusufah Allah yabaka zuriyya mai albarka da yawa" ta dad'e tana mishi Addu'a sannan yasa hannu yashare mata hawayenta yasaka rigarshi ya goge mata majina.
    Itama ta goge masa hawayen shi fuskarshi tayi jawur yana jin ummynshi fiyeda komai da kowa aduniya, lallai uwa uwace, kan cinyarta ya kwanta tana shafa sumar shi cikin so da k'auna irin na d'ah da uwa.
     Laila dake lab'e tana kallonsu kad'an zuciyarta ya tsinke saboda fargaba da tsoro.
   Kaddai yusuf zai gujeta, kar yafara son mahaifiyar shi, aranta take cewa bantab'a  ganin hawayensa ba sai yau tin bayan yana jinjiri.
No bazai yuba idan Yusuf ya gujeni yazanyi da raina nima ina sonshi fiyeda kowa Yusuf d'ana ne ba ubanda zai rabani da shi se mutuwa.


ASEEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI