FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 3⃣9⃣

"Gaskiya wannan girkin baimun ba meyasa tuwon yazama brown gabad'ai" laila dake jin shi tace "toh son kaci wannan shinkafar dama yaushe wannan k'aramar yarinyar zata iya maka girki yanda akeso" bingyal ta fusata ainun sedai kuma batace komai ba.
    Gefe ya ture plate d'in.
Laila ta zuba mishi shinkafa da miya da salat, yaci abunshi  se buga santi yake.
Bingyal tace "sis zamu wuce Allah yak'ara sauk'i" kulolin ta d'auka zata wuce dasu, Yusuf yadakatar da ita da cewa "ina zaki dasu"? kamar bata jishi ba tacigaba da had'awa.
    Laila  tace da ita "ke bakya jinsa ne"? Se a lokacin ta d'ago ta kallesa, "zan maida su gida kaci mai dad'in" ta nuna raihan "kinga sis karma kik'ara tunanin zan sake kuskuren dafa muku abinci kunada kuku kunada wanda sukafini iyawa".
   Laila ta bud'e baki "to fah yau nakejin marar kunyar yarinya, mijin 'yar uwarki kike fad'awa magana, inbanda shiririta me son zaiyi da girkin ki" juyowa tayi tana fuskantar laila "ki tambiye shi meyakeyi dashi".
    Yusuf yadaka mata tsawa "karki kuskura kigayawa uwata magana sena yi daga_daga dake anan gurin marar tarbiya kawai" raihan ta sauko kan gado tana bashi hak'uri, laila kuwa sai murmushi take.
    Tin daga ranar bingyal ta d'auke k'afarta zuwa asibitin.
  Koda gwaggo ta nemi jin ba'asi se cemata tayi bakomai tagaji ne da yawon, hakan ta kyaleta badan ta gamsu ba.
      Atare suka shigo asibitin da gwaggo kowanne yana kunyar wani karo na farko da suka fara had'uwa da juna a matsayin su na sirakan juna.
    Ummy da gwaggo kenan.
        Acikin nutsuwa da kamala tareda kunya irin ta fulani suka gaisa da juna, suna tambayar jikin raihan.
      Da murna raihan ta tare su tana musu sannu da zuwa, kowannen su yamata ya jiki, suka cigaba da fira acikin yarensu na Fulani, wanda ni asiya ba jin yaren nake ba.
     Nurse's suka shigo aka d'ibi jini da fitsarinta sukayi gwaje_gwaje sannan suka d'auko file d'in ta aka mik'awa faruk, ya dad'e yana nazari kana ya mik'awa Allah lamarin da Neman zab'insa.
      K'arfe 6 na safe wayar faruk ta tayar dashi daga bacci, yana d'agawa mezai ji sai kukan baby dasauri ya janye wayar yasake dubawa sunan faruk ne a kan wayar yasake d'aurawa a kunnensa faruk yayi dariya "congrat aboki munsamu baby boi like you" Yusuf yatashi zaune.
      "Please faruk bana son wasa raihan ta haihu ne d'an wata bakwai ya akayi"? faruk yace "kazo anan ne zaka samu amsar tambayoyin ka" dasauri sauri ya shirya ya nufe asibitin faruk.
    Sedai jikinshi yayi sanyi ganin cs akayiwa raihan.
    "Faruk meyasa zaka mun haka kayiwa matata cs batareda amincewata ba ko shawarata" faruk yadafa yusuf   "calm down Friend bamuda wani zab'i daya wuce mucire cikin inhar muna buk'atar lafiyar raihan da rayuwar d'an cikinta, sanarda kai za'ayimata cs zai saka cikin damuwa da sauran 'yanuwa dalilin dayasa na yanke shawara yimata aiki kenan batareda sanin kaba ina fatar banyi kuskure ba".
   Yusuf yayi murmushi "na yarda da kai abokina, ina fatar duk suna lafiya" faruk ya karb'a "lafiya lau suke kamar ba amata cs ba sedai yanzu tana bacci babyn kuwa yana a kwalba gaskiya bazamu bayarda shiba seyayi wata biyu sannan ne yacika mutum".
    Waya yaciro yakira laila ya shaidamata sannan yakira Abdul yayan raihan.
   After one hour.
     Hospital d'in cike da mutane 'yan uwa masu zuwa dubin raihan.
    K'arfe 9:00am ta farka da sunan Allah abakinta, ta shafo cikinta taji babu, mafarkin datayi ne yatsaya mata cak, sai muryar faruk tadawo da ita, "madam ya jikin, babynki nanan k'alau" ido ta lumshe tasake bud'ewa "na haihu kenan d'an wata bakwai zai rayu kuwa?.
     Faruk yace "mezai  hana indai yana samun kulawa babyn ma yanada girma kamar ba d'an seven month ba maybe ko one month yak'ara semu fitar dashi a kwalba" ta zare ido "kwalba kuma anan aka sakashi"? "Eh raihan karki damu komai zaizo yanda akeso".

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI