FULANIN BIRNI

🌲FULANIN BIRNI 🌲

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE3⃣1⃣

Raihan
"Anti salma gaskiya nagaji da cin wannan abun cikina zai lallace ina son ruwa fah kuce dole se wannan tsimin" anti tunba ta bita da harara "kyace kin gaji saboda baki san gatan da muke miki ba darajarki kenan agun mijiki, yanzu ma kishirya cin kwai tara da miyar zogale."
   "Menene kuma"?
"kwai ne na budurwar kaza ta hausa aka samu kwanta na fari aka ciro kwaya tara aciki sune aka dafa miki da yajin mata da, sannan akayi miyar zogale wadda taji wake, ko ahaka ma kika tsaya kin more kedai kawai idan ankawo kiyi k'ok'ari kicinye idan na shane ki shanye zakiga amfanin hakan."
    Sati biyu kenan an hana yusuf ganin amaryar tashi ba yadda baiyi magiya da sintirin zuwa gidan su ba amma fafur anti salma tace bata san zancen ba.
    Gida kuwa kowanne bangare acike yake da mutane hakama gidan su yusuf danginsu na binji sunzo da yawa.
   Dady kuwa tarasu yayi yace sukawo mishi list d'in duk wani abu dasuke buk'ata kan lokaci ya k'ure, ummy ce tayi magana da cewa "inaga yaka mata abawa kowanne bangare kud'in shi ya had'a dik abunda yake so abunda yazamo dole ayi tarayya aciki kuma se ahad'a kai koya kukace"? Laila ta gyara zamanta "ehh wannan shawara ce but ni aganina a d'auko 'yan togo da 'yan ghana sukad'ai sun isa su tsara kowani abu da ake buk'ata na bikin kuma zasuyi komai kan tsari yadda akeso" da wannan shawarar suka kwana.
      A gidan su raihan kuwa bawani d'an aiki danginsu na kebi ne zasu yi komai tareda taimakon anti salma, Dana event d'in ba yawa dinner wadda za'ayi ran d'aurin aure bayan angama walima se party wanda amarya da ango suka had'a, sekuma mother's day.
     A bangaren ango kuwa k'awayen shi sun had'a mishi rantsatstsen party nagani na fad'a , twins ma basuyi k'asa a gwuiwa ba gurin had'a Fulani's day, ummy da laila suka had'a tasu walima, atakaice dai za'ayi barin naira a bikin.
    Kaduna ta iza akayomata d'inkin da zata saka, wasu kuma a Senegal, bikine na manya yayan fillo bikin fura da nono, shanu keta ambaliya a garin sokoto kindirmo kuwa sedai kasha abarshi.

     Ba k'aramin had'uwa gurin yayi ba mayen decoration ne akayi wanda komai na gurin green ne , baban hoton sune ke maka welcome wanda sukayi acikin shigar Indian dress sunyi kyau sosai.
     Amarya da ango sukazo acikin wata k'atuwar mota faruk ke driving tareda surayya ango kuwa yana manne da amaryar shi wadda tayi kusan gigitashi tsabar kyau da taushin fatarta kyace yanzu tazo duniya, duk motsi zaice "yadai? Sedai tamishi murmushi kurum maganar ma yau wuyarta akeji.
         Doguwar rigace d'in kin bride silver color da takalminta da purse dik silver hakama head d'in ta da sark'a, angon kuwa shigar farar shadda yayi wadda ta k'ara fito da asalin kyanshi, jama'a da yawa suna mamakin had'uwa irin na angon da amarya sunyi mach sosai.
     Dollars ake zubawa malam aranar gwanja yasamu kud'i bana wasa ba.
    Ban hango muku auta ba se a yanzu, babyn badai gayuba tareda close friends d'in ta yesmin da basma haka suke tamkar tagwaye shiga kala d'aya sukayi cikin wani bowel less maroon color da ratsin red color aciki sarka da takalmi zuwa purse dik red ne se head d'in su dasukayi nad'i duk inda sukaje idon jama'a na kansu.
     Haka dai aka jera Sati d'aya ana rusar biki da wargaja dollars dik inda kaje zancen bikin zakaji anayi.
    A Fulanis day ne sukayi kusan kasheni zokuga haduwa da gashi aranar ba wanda yayi wata shiga seta Fulani har angon da amarya sunyi al'adunsu sosai , bingyal ce tabada tarihin amarya acikin harshen fulatanci sannan tak'ara da English kowa kallonta yake cikeda sha'awa yanda take fitarda vocabulary abakinta kamar bata tab'a hausa ba.
     Ta burge mutane dayawa inda samari sukayita kawo hari tana korarsu.

1st Jan /07.
Dubban mutane suka shaida d'aurin auren raihanatu Adam kebi da angonta yusuf kabir binji, se fatan zaman lafiya mai dorewa da zuri'a d'ayyaba mai albarka.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI