Posts

Showing posts from December, 2017

Fulanin birni

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 3⃣0⃣ Yusuf "Gaskiya surayya ta iya had'a girki irin wannan delicious haka anya zan iya driving kuwa" Raihan dai sai dariya take tana mamakin yanda yake ta zubawa cikin shi kamar bashi keci ba, yajawo jug d'in zobo dayaji pineapple yafara kurb'a nanma lumshe ido yayi.    "Babyna mijin surayya ya huta, but nasan dai kinfita iyawa." "Umm baby kenan ai a gidan nan kowa ya iya girki bazaka banbanta hannun raihan da surayya ba bare na auta kuma gwaggo bata barinmu bacci semun shiga kitchen everyday."     "Amma baby ai auta bata iya ko dafa ruwan zafi ba she's too young fah" raihan ta ware ido "tab ga girkinta kana ci harda santi."    "What ya fad'a tareda maida spoon a plate".    Raihan tayi dariya "yes itace ta girka surayya na wani aikin har zob'on itace tayi yakaji girkin nata ne."     Murmus...

Fulanin birni

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE2⃣9⃣ Cikin isa da k'asaita irin na laila take jifanshi da mugun kallo, wanda yadad'e baiga irinshi ba, kanshi ak'asa zuciyar shi ta soma bugawa "menayiwa Ammty na take min wannan kallon mai d'auke da tuhuma" muryarta ta katse mishi tunani da cewa "Son kana kokonto akan soyayyar danake maka? meyasa nakasan ce abun b'oye sirri a 'yan kwanakin nan meyasa na zama abun rufe sirri agareka, an kamani da wani laifin kokuwa kagan canji a gurina kodai kanason komawa mahaifiyar Kane lokacin dana gama d'awainiya da kai naci kashinka naci fitsarinka ciyonka yazamo nawa banida wani sukuni matuk'ar bakada k'oshin lafiya."          Yusuf ya d'ago sexy eye's d'in shi yace "Ammaty nayi miki laifi ne kike min gorin kulawa baki tab'a fad'ar haka ba, ammaty bana boy'e miki sirrina sedai ko idan nasan cewa zai iya zama damuwa...

Fulanin birni

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 2⃣8⃣ Gwaggo "Yaka mata aje kebi a d'ebo 'yan uwa masu muhimmanci ayi tsare_tsaren bikin nan dasu."        Tunba ta girgiza kai tana shan rake, "haka ne gwaggo, amma abari zuwa two weeks haka zanje da kaina tareda amaryar musanadar dasu daga baya se atura driver yad'auko su, inna dije da saratu se inna inno, kinga dukansu sunada wayewa ta yau da kullum a hannunsu kad'ai zaki bar Raihana su gyarata ni zanji da gyaran jikinta.     Gwaggo tayi murmushi "wannan shawarar tayi lokaci na tafiya duka yau saura kwana nawa" Raihan ta murguda baki "akwai wata d'aya fah ko yanzu sewani zumud'i kuke zan bar muku gida."     Ga bad'ayan su suka Samata dariya. Tunba tace "ke in banda abunki ai gata ake miki gidan mijinki kama da mi, ta tab'e baki "gidan ubana ma kama da me yake."      Sallamar shi ce ta maid...

Fulanin birni

🎄 FULANIN BIRNI 🎄 © ASISI B. ALEEYU ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION PAGE 2⃣7⃣ 28/Dec/07. Aunty salma ta sauko daga gombe zuwa sok. da d'an k'aramin cikinta, murna gurin su raihan ba'a magana kamar zasu cinyeta saboda murna, se girki aketa faman had'a mata kala_kala Abba kuwa yarasa inda zai sakata, Abdul yace "Tunba kinganki kuwa kin zama babbar mace wlh dubeki dubi gwaggo, kamar yaya da k'anwa"   Kwanaki k'alilan da zuwanta ta zaga dangi suka d'au hanyar Jidda tareda amincewar mijinta, acan suka kwaso kayan kitchen da Royal bed zuwa butterfly d'in kujeru abun dai sai wanda yagani komai silver color akayi, sati biyu suka dawo.    Tuni suka d'au hanyar soyayya da kwarewa irinta yusuf, kulawa yake bata na musamman gawani riritata da yake uwa uba yanda ummy kesonta zuwa yanzu har waya suke da juna hakama su usaina, atak'aice dai zumunci ya k'ullu atsakanin su.   Yau first Nov yau takama ranar birthday d...