FULANIN BIRNI

🎄 FULANIN BIRNI 🎄

© ASISI B. ALEEYU

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

PAGE 4⃣

Yusuf kabir binji.
Asalin sunan shi mahaifinshi da mahaifiyar shi duk 'yan binji ne, local government  d'in sokoto state.
     Asalin su Fulani ne na usuli auren had'i ak yiwa iyayen shi hajiya Aisha binji da Alh kabir binji.     
    Mahaifin kabir malam Ard'o binji yana d'aya daga cikin manyan garin Wanda yatara shanu bila adadin da gonaki.   
    Mahaifiyarshi modibbo ce tana koyarda yara ciki harda Aisha wadda suke cewa indo yar fillo.
'Yar kanin Ard'o ce malam Ali d'an hullo zumuncinsu gwanin sha'awa dayake kowannensu nada nashi bamai nema gurin wani. Kabir shine babba gurin mahaifiyar shi yanada k'anne biyu mata zuwaira da zubaida.
    Se yayyen shi 'yayan matar uban shi wadda itace babba tanada 'yaya biyu maza mace daya amina itace auta nuru shine babban su agidan sannan murtala se kabir maza uku mata uku.
       Kabir shine yad'auko halayen mahaifinshi sosai yana taimaka mishi zuwa gona da gurin kiwo sauran kuwa inba garari da d'aukar magana ba babu abunda suke.
Ganin suna Neman b'ata mishi  suna yabasu umarnin fiddo mata domin yayi musu aure tunda dai basa son karatu daga sabke Qur'an suka bar karatu boko kuwa ko Junior weac basuyi ba suka watsar abun na matuk'ar cin ran mahaifin , Abu d'aya ke sanyaya mishi rai ganin kabiru yadage sosai yayi littafan addini da dama yana kuma zuwa boko harya kai ss2.
Yanada son karatu sosai tareda goyon bayan mahaifiyar shi, wadda kejin ajikinta cewa zai zamo insha Allah.

     Rashin kunyar da modibbo ke yiwa kabiru da shak'uwar su tasanya tasalla uwargidan Ard'o da 'yayanta suka tsanesu dama can tana kishinta ganin yanda tazo tayi kane kane da gida daga zuwanta malam ya mallaka mata bukkar gero da sauran kayanshi itake fitarda abincin da za'a dafa Kullum ta mayar tarufe sannu sannu girkin yakoma hannunta , tasallah kuwa ta maida hankalinta ga sana'arta ta kayan gwanjo da ake saro mata ba laifi tana samu dashi take yiwa kowa gadara tana biyawa 'yayanta buk'atu.
    Modibbo kuwa koyar war datake tana taimaka mata kwarai saboda tana samun ihisani sosai gun iyayen yara na sabulu zannuwa dasauran su dashi take k'ara taimakawa kabiru yana biyan kudin makaranta yanzu haka yafara asusun zana jarrabawar kare makaranta ta biyu.
     Yaune ake d'aurin auren nuru da murtala gidansu yana bayan gidan maigari Wanda yake ahad'e , arashi da gori babu Wanda modibbo bata shaba , bata kula suba tacigaba da hidimar da ake zuwaira 'yarta da ke auren maigari wadda itace ta hud'u tarik'a k'unk'uni danme za'a raina musu uwa modibbo tace.
    "Kul na k'ara jin bakinki, ba uwar ki ba ce in yau na mutu kinada uwane bayan ita" zubaida dake damun fura tace.
   "Haba modibbo sabida Allah fah kina ganin yanda suka rainamu wallahi Allah.
   Hararar data bita da ita yasakata yin shiru badan taso ba , kabiru yashigo da uniform d'inshi dasuka kod'e amma fah tas suke, yagaida mutan gidan yaje d'akinsu yacire yafito fuskar shi cike da fara'a "innata yau nagama jarrabawa sejiran sakamako zuwa wata shekara kafun nan natara kud'in registration d'an fodio zanje insha Allah.
    "ldan dai nasamu naci jam d'ina yadda akeso" zuwaira tace "ai kuwa mud'inma asusun zamuyi gomna Muke son kayi ka gyara mana garin nan " zubaida ta kyalkyale da dariya " gaskiya kam babban yaya yazama gomna ai lafiyar Mu k'alau.
      Inna najinsu tamusu banza shikam hankalinshi naga modibbon shi ya zura mata ido itakuma se wani kaucewa take , zuwaira tace
   "K'anwa mubasu guri uwa da d'anta, inaga sirri zasuyi wannan kauda idon , bata k'arasa ba inna modibbo takai mata dundu "marasa kunya nida ke ne" suna dariya suka bar gurin.
   Suna fita yak'arasa gurin inna modibbo yace " inna ta yaya ake ciki ni yunwa nakeji , ya kukayi da indo"? Inna modibbo tace " kaje idan kaci abinci kadawo,  munyi maganar da malam yaji dad'i sosai zumunci zai k'aru , ga yarinyar mai nutsuwa da hankali , nikaina tin bayau ba nake kwad'ayinka da ita.    murmushi yayi "kicigaba da samana albarka da Neman zabin Allah.

ASEEYAH BASHEER ALEEYU

Comments

Popular posts from this blog

FULANIN BIRNI

Fulanin birni

FULANIN BIRNI