FULANIN BIRNI
🎄 FULANIN BIRNI 🎄
©ASISI B.ALEEYU
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
PAGE1⃣
Da sunan Allah mai rahma mai jinkai
Sallama akayi da wata k'aramar murya mai kama da rera wak'a , matar dake zaune kan k'war yar nono tayi murmushi tareda maida ludayin icce ta rufe da murfin kaba.
"Amin wa'alaki sallam bingyaal jam waali koh. Wadda aka kira da bingyaal ta gyada kai.
"Jam taan gwaggo aba selli naa.
"bingyaal jam ni kwasam fah.
bata fuska tayi zata fara zubo da hawaye.
"gwaggo ni pizza wallahi.
gwaggo ta bude baki "da pizza zakiyi Karin kumallo ina mukaga pizza yanzu in zaki sha kisha in ba haka ba zan tad'o yayanki kinsan halinshi.
baki ta zunbure
"toh cheese fah" .
sake da baki take kallonta.
"kinga babu ko d'aya jeki kitchen kidubo mekike so.
Hawaye ta soma yi da basu da dalili gwaggo ta bude furarta tacigaba da sha.
hakan yak'ara bata mata rai tuni tasa kuka , kukanta ne yatashe sisters d'inta.
su biyu suka sauko downstairs kowacce tana mik'a alamar baccin ya ishesu ta bayan ce tafara magana a harshensu na Fulani dani bangama k'warewa ba bare nagane mesuke cewa,
d'ayar tacirata sama suna yawo a falon tana mata magana a Hausa sannan naji.
"me akayiwa auta babbar auntynmu?
k'ara lafewa tayi ajikin yayar tata tana mata nuni da gwaggo
"wai gwaggo ce pizza waala cheese ma" dariya yayar tata tayi
"bingyaal kinfi kowa sanin k'a'idar gidannan amma kina son karyewa bazaki sha nono ba sabon ta tsaa ne"
"Abadan" tafad'a da k'arfi d'ayar ce ta karb'eta tace "fresh yoghurt ? Laban ? Fresh milk ?
Murmushi tayi milk , "OK baby kori baa si fuu waala?
"Yup ikhtee jam tan baa fuu waala"
Peck ta mata a fuska ta diro k'asa tana yiwa gwaggo gwalo ,
"wallahi gwaggo Abba fuuu fuuu"
dariya tayi ta gyada kai.
"bingyaal Allah moyyin laawol" Ameen suka amsa tare.
se alokacin suka gyaida ita, sannan suka fara shan furar dataji nono da k'ank'ara kowanne ya zuba a k'aramar k'warya mamaki yacikani wai breakfast da fura baki na tab'e abun ajini yake fillo da nono jini da anta ne
Bayan kamar awaya d'aya naji hayaniya lek'awa nayi dan naga meke faruwa.
yaya Abdul_rahman ne babban yayansu, kuma tilo tak a maza,
"how dare you Ali how many hours dana d'auka Ina jiranka kace min baka wanke motar nan ba, ashe ban gayamaka inada muhimmiyar fita ba"
"Sorry sir" ya fad'a yana mai rank'wasar da kanshi.
"wlh ciyon nan ne nawa yatashi bakaji bane dasafen nan nadawo daga asibiti banma San hashimu yakaini ba, koyanzu matsawa nayi a sallameni saboda nasan yanda mukayi dakai jiya amun afuwa"
Lafe take a kafad'ar yayan nata tace "bandirawo Ali selli Waala fah afuwan koh " murmushi yayi ya lak'ato hancinta "baby hot stuff Allah b'oydu jam "
"Amin my charming and adorable big bruh" ta lek'o da 'yar pretty face d'inta.
"Ali ka koma asibitin ka kira hashimun ya wanke mana but quickly fah muna jira"
hannu ta zira a aljihun yayan nata taciro rafar d'ari biyar da alama an tab'asu.
"kayi manage dasu zamu zo letter be very care full, kasan ciyonka na buk'atar kulawa sosai , inaga za'a turo d'aya daga ma'aikatan gidan nan a kula da kai , maza ka koma.
Takalli yayanta "right ko ?ya lak'aci hancinta "rightly lil sis that's why you're different in thousands girls include your sisters.
" Allah yabaki mini nagari "
Dariya tayi ta rufe fuska.
"Same with you bro kaima Allah ya baka mar'atu saliha Ameen.
Mamaki yacikani ganin wannan yarinyar yar 15 amma tanada zurfin tunani da sanin ya kamata, ko dayake turban da iyayenta suka d'orata kenan.
Banajin ko bayan ransu halayen ta zasu canza , sai dai ikon (Arrahman )
'Yan uwa mata da iyayenmu k'alubale ne agaremu akan tarbiyar yaranmu , yaro tin yana aciki ake tarbiyar shi karkice wai seta girma ba haka abun yake ba.
Kugane tarbiyar ma kala _kala ce tarbiyar magana , tarbiyar cin abinci tarbiyar girmama manya dasauransu .
Tarbiyar yaro idan yana aciki ta had'a da kiyaye cin haram rage yawan magana musamman idan ba mai amfani bace.
barin k'arya kiyaye dokokin Allah da manzonsa yawan yimasa adduar tsari da kuma nema mass shiriya gurin ubangiji ,
inaga cewa idan kika kiyaye wannan kin faro daga k'asa kin yiwa yaronki foundation mai kyau wanda bana tunanin agaba zai zube
ASEEYAH BASHEER ALEEYU
Comments
Post a Comment